'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

  • Rundunar yan sanda a Jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutane 29 ne aka nema aka rasa bayan harin da yan bindiga suka kai kauyen Ruwan-Godiya
  • Maharan sun kai harin ne a daren ranar Lahadi inda suka isa garin dauke da muggan bindigu suka rika harbe-harbe a iska don tada wa mutane hankali
  • Gambo Isah, kakakin yan sandan Jihar Katsina ya ce an tura karin jami'an tsaro zuwa kauyen da nufin ceto wadanda aka sace da tabbatar da tsaro

Jihar Katisina - Jimillar mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kaduna: An kashe mutane 5, an ƙona gidaje da dama a sabon harin da 'yan bindiga suka kai a Atisa

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
'Yan sanda su tabbatar da sace mutum 29 a wani kauyen Katsina. Hoto: Channels Television
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Isah, yayin da ya ke bayyana matakan da yan sandan suka dauka, ya ce tuni an tura tawagar jami'an tsaro zuwa yankin domin ceto mutanen kauyen da aka sace.

Ya kuma ce akwai yiwuwar wasu daga cikinsu ba sace su aka yi ba, sai dai sun tsere sun shige cikin daji ne kuma suna kokarin koma wa gida.

Kakakin yan sandan ya ce:

"An rahoto cewa mutane ashirin da tara aka sace a garin duk da cewa akwai yiwuwar wasu sun tsere ne kuma suna kokarin koma wa gida.
"Amma, mun kara adadin jami'an tsaro, ciki har da yan sanda masu sintiri a garin yayin da muke kokarin ganin an ceto dukkan wadanda aka sace."

Kara karanta wannan

Yadda 'yan awaren IPOB suka halaka makiyayi, suka bindige shanu 30

An samu sabani kan adadin mutanen da aka sace

Yayin da rahoton sace mutanen daga Ruwan-Godiya ke bazuwa, wani shugaban al'umma a kauyen, Mohammed Murtala, ya shaida wa Channels Television cewa ba a ga mutum 38 ba bayan harin.

A cewar majiyoyi, yan bindigan sun afka garin dauke da muggan makamai kan babura fiye da 60.

An ce sunyi ta harbe-harbe a iska don tada hankalin mutane, duk da cewa akwai sojoji a garin.

Obasanjo: Sai an binciko kuma an hukunta wadanda suka banka wa gona ta wuta

A wani rahoton, Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alawadai akan kona gonarsa da wasu batagari suka yi a garin Howe da ke Karamar Hukumar Gwer ta Kudu a Jihar Binuwai a kwanakin karshen makon nan, The Punch ta ruwaito.

Tsohon shugaban kasar mai shekaru 84 ya kwatanta lamarin a matsayin mummunan abu kuma ya ce sai jami’an tsaro sun gano wadanda suka tafka ta’asar.

Kara karanta wannan

Katsina: An kama boka da ke yi wa 'yan bindiga asiri da addu'oin samun sa'a

The Punch ta ruwaito yadda batagari suka babbake gonar Orchard wacce mallakin babban mutumin ne na Hilltop da ke Abeokuta a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel