Karin bayani: 'Yan fashi sun yi awon gaba da motar kudi, sun kashe 'yan sanda 2

Karin bayani: 'Yan fashi sun yi awon gaba da motar kudi, sun kashe 'yan sanda 2

  • 'Yan fashi da makami sun farmaki wata motar banki a jihar Oyo, inda suka hallaka 'yan sanda har biyu
  • Lamarin mara dadi ya faru ne jim kadan bayan da motar ta fito daga wani banki da ke kusa da yankin
  • Rundunar 'yan sanda bata tabbatar da lamarin ba, amma majiyoyi sun ce da gaske lamarin ya faru a wata unguwa

Jihar Oyo - An samu tashin hankali a ranar Alhamis yayin da wasu ‘yan fashi suka farmaki motar kudi a unguwar Idi-Ape da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, The Nation ta ruwaito.

Wasu majiyoyi da ba a tantance ba sun ce ‘yan sanda biyu sun mutu yayin da ‘yan fashin ke harbe-harbe a lokacin da suke gudanar da barnar.

'Yan fashi sun barnata motar kudi
Yanzu-Yanzu: 'Yan fashi da makami sun farmaki motar kudi, sun kashe 'yan sanda | Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter

Ba a iya tabbatar da ko ‘yan fashin sun yi nasarar yin awon gaba da motar kudin ba, duk da cewa wasu rahotanni sun ce an tafi da motar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suke Bakin Aikinsu

Wasu majiyoyi sun ce motar kudin ta fito ne daga daya daga cikin bankunan da ke kusa da inda lamarin ya faru.

Kokarin tabbatar da faruwar lamarin daga ‘yan sanda ya ci tura, domin ba a samu jin ta jami'an hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Oyo ba.

An tafi da motar kudi

A bangare guda, wata majiya ta shaida wa jaridar Punch cewa, 'yan fashin sun tafi da motar, amma ba a iya tabbatar da batun ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, saboda ba a samu bayani a hukumance ba.

Majiyar ta ce, mazauna garin da masu ababan hawa da ke gefen titi sun gudu sun buya don gudun kada ‘yan fashi da makamin su harbe su.

Ya kara da cewa, ’yan sanda daga rundunar ‘yan sandan yankin, a titin Iwo sun zo wurin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC

'Yan bindiga sun tare motar kudi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kudade

A wani labarin, wasu yan fashi da makami dauke da bindigu sun farmaki motar dakon kudi ta wani Banki da har yanzun ba'a gano ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun samu nasarar fasa motar, kuma sun yi awon gaba da adadi mai yawa na kudi a kan hanyar Otor-Owhe, karamar hukumar Isoko North, jihar Delta.

Yan fashin sun bude wa motar wuta ba kakkauta wa har sai da Harsasan bindiga suka fasa wawukeken rami a sashin motar dake dauke da kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel