Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

  • Yan fashi da makami sun farmaki motar dake ɗakko kuɗi ta Banki, sum kwamushe makudan kuɗaɗe a jihar Delta
  • Rahoto ya nuna cewa yan fashin sun fasa motar da harsasan bindiga, yayin da suka ɗibi kudi suka yi gaba
  • Har yanzun babu cikakken bayani kan adadin kuɗin da suka sace, kuma babu bayani kan motar wane Banki ce

Delta - Wasu yan fashi da makami ɗauke da bindigu sun farmaki motar dakon kuɗi ta wani Banki da har yanzun ba'a gano ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun samu nasarar fasa motar, kuma sun yi awon gaba da adadi mai yawa na kuɗi a kan hanyar Otor-Owhe, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta.

Motar dakon kudi
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe Hoto: naijauto.com
Asali: UGC

Yan fashin sun buɗe wa motar wuta ba kakkauta wa har sai da Harsasan bindiga suka fasa wawukeken rami a sashin motar dake ɗauke da kuɗin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Daga Sokoto, Shugaba Buhari ya fasa zuwa Zamfara saboda yanayi ba kyau

Motar ta wane Banki ce?

Har yanzun da muka tattara wannan rahoton, ba'a bayyana motar ta wane Banki bace, kuma ba'a bayyana ainihin adadin kuɗin da maharan suka sace ba.

Kazalika ba'a tabbatar ko an rasa rayuka ba yayin wannan harin, duba da cewa motar na tafiya da yan rakiya daga jami'an tsaro.

Duk wani kokari na samun kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, ya ci tura, domin wayarsa a kashe take, kamar yadda Tribune ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai hari Sakatariyar APC yayin da mambobi ke zanga-zanga a Ekiti

An shiga tashin hankali a jihar Ekiti kan cece-kucen da yaƙi karewa wa game da zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

Wasu tsageru sun fara harbe-harbe a babbar Sakatariyar APC yayin da mutane suka taru suna zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel