Karin bayani: 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suke Bakin Aikinsu

Karin bayani: 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suke Bakin Aikinsu

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka wa wasu yan sanda da ke aiki a titi sun bindige guda uku har lahira
  • Yan bindigan sun bude wa yan sandan wuta ne a timber junction, kusa da Maryland a karamar hukumar Enugu ta kudu a ranar Alhamis
  • Bayan kashe yan sanda guda uku, da jikkata wani direban adaidaita sahu, miyagun sun kuma yi awon gaba da wata mata tare da direbanta

Enugu - Hankula sun tashi a ranar Alhamis a yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka bindige yan sanda uku har lahira a shingensu a Enugu.

Lamarin ya faru ne a kan timber junction, kusa da Maryland a karamar hukumar Enugu ta kudu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan fashi sun yi awon gaba da motar kudi, sun kashe 'yan sanda 2

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Harbe 'Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suka Bakin Aikinsu
Yan Bindiga Sun Bindige Yan Sanda 3 Har Lahira Yayin Da Suka Bakin Aikinsu. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gano kuma ce bata garin sun sace wata mata da direban ta a wurin.

Vanguard ta gano cewa wani direban Keke Napep ya jikkata sakamakon harsashin da miyagun suke ta harbawa daga bindigansu domin su firgita mutane.

Rundunar ta tabbatar da afkuwar harin

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Enugu ya tabbatar da afkuwar lamarin duk da bai bada cikakken bayani ba.

Ya ce yan sanda sun bi sahun yan bindigan

Ya ce:

"Har yanzu ba mu gama tattara bayani dangane da afkuwar lamarin ba. Amma dai an tura jami'ai domin su bi sahun miyagun."

Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Man fetur lita milyan 300 ya dira Najeriya, NNPC

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel