Hotuna: Mai kishin jama'ar karkara ya gina makaranta a kungurmin kauyen da basu san Boko ba

Hotuna: Mai kishin jama'ar karkara ya gina makaranta a kungurmin kauyen da basu san Boko ba

  • Wani mutum a jihar Gomne ya kalubalanci yadda ilimi ke tabarbarewa, ya gina makaranta a rugar Fulani
  • Ambasada Habu Ibrahim Gwani, ya gina makaranta mai azuzuwa guda biyu da ofis daya, inda ya mika ta ga gwamnatin domin a kula da ita
  • Wannan lamari ya yi matukar daukar hankali, inda gwamnati ta turo wakilai domin yabawa wannan bawan Allah

Yamaltu Deba, Gombe - Yayin da mutane da dama ke koka yadda gwamnati ta gaza wajen tabbatar da ingantaccen ilimi ga alummar kasar nan, wani mutum a jihar Gombe ya zo da sabon tsarin habaka ilimi.

Ambasada Habu Ibrahim Gwani, wani mazaunin jihar Gombe ne da ya gina wata makarantar firamare a wani kungurmin kauye mai suna Agangaro da ba kowace irin mota ce ke iya shiga ba.

Kara karanta wannan

Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai

Ambasada Habu Gwani ya gina makaranta ga Fulani
Hotuna: Wani mutum ya gina makaranta a kungurmin kauyen da basu san Boko ba
Asali: Depositphotos

Kauyen Agangaro, wanda hedkwata ne ga wasu rugagen Fulani a yankin Gwani yamma ta karamar hukumar Yamaltu a jihar Gombe, a zagaye yake da mutane da dama, wadanda ke rayuwa ba tare da sanin yadda ake karatu da rubutu ba.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe, ya yi tattaki wajen taron budewa da mika makarantar ga gwamnatin jiha har wurin da aka yi ginin, inda ya tattaro bayanai tare da tattaunawa da mutumin da ya yi wannan aikin.

An yi bikin budewa tare da mika makarantar ga gwamnati a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairun 2022.

Makarantar gwani
Irin mutane da ke rayuwa kauyen Agangaro
Asali: Depositphotos

Ilimi hakkin kowa ne, ilmantarwa ba aikin gwamnati ne kadai ba

Ambasada Gwani, ya bayyana asalin abin da ya fara jawo hankalinsa zuwa gina makaranta a yankin na karkara, duk da cewa zai iya gina irin wannan makaranta a cikin gari.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa Abubakar: Gwamnatin Ganduje zata baiwa Abdulmalik Tanko Lauyan da zai kare shi

A cewarsa, irin mutanen da ke cikin dajin nan su ne suka fi cancanta a wayar dasu, su san mai kyau da mara kyau domin tsira da rayuwarsu a hannun zamani.

Hakazalika, ya ce tun farko ya yi yawo a kasashe da dama, inda ya ga cewa, duk wata al'ummar da ta tsira, to ilimi ne ya sa ta habaka zuwa inda take.

A bangare guda, ya ce yana da zimmar yakar jahilci a cikin alumma, wannan yasa ya tashi tsaye domin wannan aiki.

A kalamansa, Gwani ya ce:

"Ni tashi na, da kuma aikina da yawo na da nayi na duniya, saboda aiki na zaga kasashe da yawa, na ga duk inda na zaga a duniya, ci gabansu ya dogara ne da ilimi. Ba akan karfinsu ba, ba akan ko wani abu nasu ba, duk ilimi ne ya kawo musu ci gaba.
"Saboda haka, idan muka dawo nan wajenmu, kamata yayi mu yi hobbasa wajen ganin mun habaka ilimi, saboda dashi ne za a samu fasaha da komai ma."

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinci gawar mai gadi da iyalansa uku a wani gidan gona a Abuja

Batun mika makaranta ga gwamnati

Da wakilinmu ya tambaye shi kan dalilin da yasa ya mika wa gwamnati makarantar, da kuma abin da yake sa ran za ta yi, Gwani ya shaida masa cewa, a halin yanzu gwamnati ta karbi makarantar, saboda gini shi yafi sauki akan tafiyar da ita.

Ya ce ya rage wa gwamnati ta aiko abubuwan da za su sa makarantar ta habaka domin, a yanzu malamai biyu ne na sa kai ke lura da makarantar.

Makarantar da Gwani ya gina a Agangaro
Makarantar da aka gina a kauyen Agangaro
Asali: Depositphotos

Hakazalika, ya ce zai ci gaba da tuntubar gwamnati tare da tuna mata don tabbatar da makarantar bata durkushe ba.

Ya kuma kara da cewa, ba wai ya mika makarantar ne ga gwamnati shi kenan ya zare hannunsa a kai ba, zai ci gaba da aiki gwiwa da gwiwa da gwamnati don ganin ci gaban ta.

A halin da ake ciki, ya shaida cewa, akwai dalibai sama da 150 da ke karatu a makarantar, kuma duk shi ya yi musu surutar makaranta da komai.

Kara karanta wannan

Gombe: Bayan kwanaki 30 a kasar waje, gwamna ya dawo tsaka da rikicin siyasa

Daga karshe, ya yi kira ga masu hannu da shuni da ma sauran jama'a da su tashi tsaye domin gina al'umma a kowane wuri akan turba ta ilimi.

Bangaren gwamnati

Jami'in gwamna daga Hukumar Ilimi ta bai daya ta Jiha (SUBEB), Kwamared Sani Sabo, ya yaba da kokarin Ambasada Gwani, inda ya ce gwamnati a shirye take domin hada karfi da ganin ci gaban makarantar.

Gwani ya gina makaranta a kauyen Fulani
Yayin da ake nunawa jami'in gwamnati makarantar
Asali: Depositphotos

Sani Sabo ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin taron, inda yace zai ba da rahoto ga ofisohin da suka dace domin inganta makarantar.

A bangare guda, ya ce, bangaren BESDA za ta shigo cikin lamarin domin ganin ta inda za ta taimaka.

Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata daga haduwa da su a hanyar kauye

A wani labarin, a safiyar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya hango wasu kananan yara da su ke yawo a kan titi.

Kara karanta wannan

Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus

Wadannan yara mata biyu suna aiki ne a sa’ilin da ya kamata a ce su na makaranta kamar yadda sauran sa’o’insu suke cikin aji a daidai wannan lokacin.

Mai magana da yawun bakin Mai girma gwamnan, Gboyega Akosile ya fitar da jawabi na musamman, ya ce gwamnati ta dauki dawainiyar yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel