Kisan Hanifa Abubakar: Gwamnatin Ganduje zata baiwa Abdulmalik Tanko Lauyan da zai kare shi

Kisan Hanifa Abubakar: Gwamnatin Ganduje zata baiwa Abdulmalik Tanko Lauyan da zai kare shi

  • A zaman kotu na yau Litinin, gwamnatin jihar Kano ta amince da bukatar babban wanda ake zargi da kisan Hanifa, Abdulmalik Tanko
  • Tanko da sauran mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, sun bukaci gwamnati ta samar musu da lauya wanda zai tsaya musu
  • Alkalin kotun, mai shari'a Sulaiman Na'Abba, ya ɗage sauraron shari'ar zuwa 14 ga watan Fabrairun 2022

Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje, zata baiwa wanda ake zargi da kisan Hanifa Abubakar Lauyan da zai tsaya masa.

BBC Hausa ta rahoto cewa wanda ake zargi na farko da kisan Hanifa, Tanko, ya shaida wa kotu cewa ba shi da lauyan da zai tsaya masa a shari'ar da ake cigaba da yi.

Hanifa Abubakar da Ganduje
Kisan Hanifa Abubakar: Gwamnatin Ganduje zata baiwa Abdulmalik Tanko Lauyan da zai kare shi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Haka nan kuma, Tanko, shugaban makarantar da Hanifa ke karatu, ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta taimaka masa da Lauya.

Kara karanta wannan

Wani Saurayi ya lakadawa budurwarsa duka har ta mutu bayan ya dirka mata ciki

A zaman kotu na yau Litinin, Tanko yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba mu da lauya a yanzu. kasancewar ba mu da damar ganin kowa a tsare, ina mai rokon gwamnatin Kano ta taimaka mana da lauya."

Kazalika sauran mutum biyu da ake zargin sun haɗa baki da Tanko wajen aikata wannan ɗanyen aiki, Fatima da Hashim Isiyaku, sun amince da maganar Abdulmalik.

Shin gwamnatin Kano ta amince da bukatar su?

A ɓagaren gwamnati, Lauyanta, Lawal Musa, ya ce gwamantin Kano za ta samar musu da lauya kamar yadda suka buƙata.

Kasancewar laifin da ake zargin mutanen da aikata wa mai girma ne, doka ta tanazar da samun lauyan da zai tsaya musu.

Bayan haka, Mai Shari'a, Sulaiman Na'abba, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022 da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada belin jagoran Win/Win, Muaz Magaji

Jami'an hukumar yan sanda sun yi ram da mutane uku da ake zargi da garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar, yar kimanin shekara 5 a duniya a watan da ya gabata.

A wani labarin na daban kuma Bayanai sun fito kan tattaunawa tsakanin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Osinbajo, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Alamu masu karfi sun tabbatar da cewa jam'iyyar APC ta fara zawarcin tsagin Sanata Rabiu Kwankwaso na PDP.

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, na ɗaya daga cikin manyan yan siyasa masu dumbin magoya baya musamman a arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel