Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata daga haduwa da su a hanyar kauye

Gyadar doguwa: Gwamna ya canza rayuwar 'yan mata daga haduwa da su a hanyar kauye

  • Gwamnan jihar Legas ya yi kicibis da wasu mata da suke yawo a lokacin da sa’o’insu su ke makaranta
  • Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini za su je kai wa iyayensu markade ne sai gwamna ya hange su
  • A karshe Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi alkawarin daukar nauyin karatun wadannan Bayin Allah

Lagos - A safiyar Alhamis, 3 ga watan Fubrairu 2022, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya hango wasu kananan yara da su ke yawo a kan titi.

Wadannan yara mata biyu suna aiki ne a sa’ilin da ya kamata a ce su na makaranta kamar yadda sauran sa’o’insu suke cikin aji a daidai wannan lokacin.

Mai magana da yawun bakin Mai girma gwamnan, Gboyega Akosile ya fitar da jawabi na musamman, ya ce gwamnati ta dauki dawainiyar yaran.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan Boko Haram na taimakawa wurin yaki da ta'addanci, Zulum

Wani hadimin Gwamnan, Jibril Gawat ya bada labarin duk abin da ya faru a shafinsa na Twitter.

Labarin Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini

Dole ce ta sa Amarachi Chinedu mai shekara 9 da Suwebat Husseini ‘yar shekara 12 suka hakura da karatun boko, suka je su na taya iyayensu aiki a gida.

Mun ji cewa tawagar gwamnan na jihar Legas ta ci karo da Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini ne a kauyen Anthony da kimanin karfe 11:00 na safe.

Gwamnan Legas
Amarachi Chinedu da Suwebat Husseini Hoto: Jubril A. Gawat @Mr_JAGs
Asali: Twitter

“Yaran su na kan hanyar kai sakon bokitan wake da barkono ne zuwa wajen markade a lokacin da gwamnan ya hange su a kauyen Anthony.”
“Wannan abin ya sa hankalin Gwamna bai kwanta ba, ya bukaci motarsa ta karasa wajen yaran domin jin abin da ya sa ba su zuwa makaranta.”

Kara karanta wannan

Dukiyar sata: Yadda Ministan Buhari ya lallaba, ya ba kamfani kwangilar makudan Biliyoyi

- Gboyega Akosile.

Labarin Amaechi ya sa jikin gwamna ya yi sanyi. Mahaifiyarta malamar makaranta ce amma ba za ta iya zuwa makaranta ba saboda kudin karatu ya yi tsada.

Ita kuwa mahaifiyar Suwebat ta na saida kosai ne, don haka ‘diyar take yi mata aikatau. Asalin iyayenta mutanen Jigawa ne da suka tare a Legas kwanaki.

Sauran ‘yan uwan Suwebat maza hudu su na karatun boko, sai aka bar ta a gida domin taya mahaifiyarsu aiki, labarinta ya sa gwamnan ya ji tausayinsu.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yi alkawarin sa yaran a makaranta su cigaba da karatu kamar kowa. Tuni an sanar da iyayensu a kan matakin da aka dauka.

Martanin mutane

Wasu su na ganin cewa Sanwo-Olu ya yi wannan ne saboda ganin siyasa ta karaso kurum, tun da dai ba a taba jin labarin ya yi irin wannan aiki ba tun 2019.

Demola Rewaju, daya daga cikin matasan PDP a Legas ya soki gwamnan, ya ce abin da ya kamata shi ne a duba abin da ya hana su zuwa makaranta, ayi gyara.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan bindiga sun bindige yayan kwamishina a jihar Benue

Asali: Legit.ng

Online view pixel