Rashin tsaro: Matasa 'yan 'Yahoo' sama da 40 sun yi wa wata unguwa kawanya a Abuja

Rashin tsaro: Matasa 'yan 'Yahoo' sama da 40 sun yi wa wata unguwa kawanya a Abuja

  • An sha gumurzu tsakanin 'yan yahoo da wasu masu tsaro wata unguwa a babbar birnin tarayya Abuja
  • Matasan sama da 40 sanye da fararen kaya sun yiwa unguwar kawanya sannan suka yi kokarin kutsawa ciki ta karfin tuwo
  • Da farko masu gadin sun kora su da misalin karfe 11:45 na dare amma sai suka sake dawowa da karfinsu da misalin 2:30 na tsakar dare

Wasu matasa da ake zargin yan Yahoo ne su sama da 40 sun yi yunkurin kutsawa unguwar Mab Global Estate da ke Abuja a daren ranar Juma’a, 4 ga watan Fabrairu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wadanda ake zargin sun yi shiga na fararen kaya sannan suka yi yunkurin kutsawa unguwar da misalin karfe 11:45 na dare amma tawagar tsaro na hadin gwiwa suka hana su.

Kara karanta wannan

Wadanda suka sace yan uwan malamin jami’ar Zamfara sun nemi a biya miliyan N70

Rashin tsaro: Matasa 'yan 'Yahoo' sama da 40 sun yi wa wata unguwa kawanya a Abuja
Rashin tsaro: Matasa 'yan 'Yahoo' sama da 40 sun yi wa wata unguwa kawanya a Abuja Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Sun gaza bayar da cikakken bayani game da lambar gidan da ake tsammanin zuwansu, don haka masu tsaron unguwar suka kora su.

Sai dai kuma, sun sake dawowa a karfinsu cikin ayarin motoci 15, wanda ke dauke da mutane sama da 40 cikin shiga na kararen kaya da misalin karfe 2:30 na tsakar dare.

Wani jami’in tsaro ya ce sun fusata yayin da suka yi yunkurin shiga unguwar ta karfin tuwo.

Matasan sun kasance rike da bakaken jakunkunan da ake zaton makamai ke ciki sun ce lallai za su halarci wani taron baide ne a fili mai lamba 312 Gold na unguwar, rahoton The Sun.

Jami’an tsaron wadanda suka tsaya kan maganarsu, sun bayyana cewa gida mai lamba 312 mai zaman kansa ne ba na haya ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An bindige gawurtattun yan bindiga uku har Lahira

Amma sai yan yahoo din suka dage cewa dole sai an bude masu kofar shiga unguwar inda suka fara gwagwarmaya da masu tsaron.

Sai da wani shugaban masu tsaron unguwar, Mista Denis Omala, ya kira dukka yaransa fiye da su 50 don hana su tayar da zaune tsaye a unguwar.

Sai da daya daga cikin jagororin unguwar ya fito da tsakar daren don tabbatar da ganin cewa an kora matasan domin ba a san manufarsu ba.

Ya bukaci mazauna unguwar da su sanya idanu sosai saboda yadda ake ta kokarin yiwa tsaron unguwar kutse a baya-bayan nan.

Niger: 'Yan kauye ne ke bai wa 'yan ta'adda bayanan sirri, Sanata Musa

A wani labarin, Sanata Sani Musa, mai wakiltar gabashin jihar Niger inda 'yan bindiga suke cin karen su babu babbaka, ya yi kira ga mazauna kauyuka da matasa da su hada kawuna don ganin an zakulo gami da wartakar 'yan bindiga a jihar Niger.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

Ya kara da kira ga jami'an tsaron da su yi amfani da dabarbarun zamani wajen ganin sun yi gaba da gaba da 'yan ta'addan kamar yadda ya roki gwamnatin tarayya da ta samar da tabbataccen sansanin sojoji a yankunan da ake yawan kai hari, Vanguard ta ruwaito.

Sanatan, yayin wata tattaunawar waya da jaridar Vanguard, ya sanar da yadda wasu al'amura marasa dadi suke faruwa a jihar, inda suke nuna yadda wasu 'yan kauye suke da hannu dumu-dumu a ta'addanci, har wasu suke zama 'yan leken asirin 'yan bindigan wanda hakan ke matukar wahalar da jami'an tsaro don ganin sun sheke su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel