Nasara daga Allah: An hallaka gawurtattun yan bindiga da suka addabi mutane a kan hanya

Nasara daga Allah: An hallaka gawurtattun yan bindiga da suka addabi mutane a kan hanya

  • Yan sanda, sojoji da yan Bijilanti sun samu nasarar kashe yan bindiga uku daga cikin tawagar da ta addabi mutane a hanyar Benin-Auchi
  • Yan bindigan sun kai hari kan hanyar ranar Talata amma jami'an tsaro suka kore su, suka sake fitowa yau Laraba aka kashe uku
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Kontongs Bello, ya tabbatar da lamarin, yace ko ta tsiya sai jihar Edo ta zauna lafiya

Edo - Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwane da suka addabi mutane sun halaka a hannun jami'an tsaron haɗin guiwa da suka haɗa da sojoji, yan sanda da yan Bijilanti a Edo.

Daily Trust ta rahoto lamarin ya faru ne bayan doguwar musayar wuta a yankin Okwo dake Ehor a ƙaramar hukumar Uhunmwode, kan hanyar Benin-Auchi, jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

Rahoto ya bayyana cewa yan ta'addan sun rufe hanyar da safiyar ranar Talata, amma jami'an tsaro suka fatattake su bayan doguwar musayar wuta.

Yan bindiga
Nasara daga Allah: An hallaka gawurtattun yan bindiga da suka addabi mutane a kan hanya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kazalika yan bindigan da suka kawo harin jiya, sune suka sake toshe hanyar yau Laraba da nufin sace matafiyan dake bin hanyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma jami'an tsaro suka sake tarban su aka sake gumurzu na tsawon lokaci, yayin haka ne aka samu nasarar bindige mutum uku, sauran kuma suka ranta ana kare ɗauke da raunin bindiga.

Shin sun taba wani farar hula?

Rahoton da muka samu ya nuna cewa babu wanda maharan suka illata, in banda wani Alburushi da ba'a san daga inda ya fito ba ya sami direban wata SUV a kafaɗa yayin da motoci ke jira na tsawon awanni.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Edo, SP Kontongs Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki jigon APC, sun sace shi tare da wasu mutum hudu

Vanguard ta rahoto Kakakin yan sandan yace:

"Eh, dagaske ne lamarin ya faru jiya Talata, amma jami'an haɗin guiwa na yan sanda da sojoji sun daƙile hari, babu wanda yan ta'addan suka sace, mutum.ɗaya ne Alburushi ya same shi a kafaɗa."
"Yau Laraba, yan bindigan suka sake fitowa su addabi mutanen kan hanya, amma jami'an tsaron haɗin guiwa suka halaka mutum uku. Dole Edo ta zauna lafiya."

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya tabbatarwa yan Najeriya cewa cikin watanni masu zuwa za su ga gagarumin canji na cigaba

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa yana sane da alƙawurran da ya ɗauka a shekarar 2015.

Shugaban yace cikin yan watanni kaɗan masu zuwa, mutane za su ga gagarumin canji a arewa maso gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel