Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani

Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani

  • Kungiyar malaman jami’ar ta ASUU reshen Jami'ar Bayero Kano (BUK) ta ce ba za a gudanar da laccoci a jami’ar ba a ranar Litinin 7 ga watan Fabrairu
  • A cewar ASUU, an dauki matakin ne domin wayar da kan dalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki kan gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu
  • A halin da ake ciki, ASUU a baya ta ce ta gaji da ganawar da take yi da FG ba tare da cimma wata manufa ba, kuma ta yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar

Jihar Kano – Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK), ta ayyana ranar Litinin 7 ga watan Fabrairu a matsayin ranar hutu a jami’ar.

Kara karanta wannan

Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta ce za ta yi amfani da wannan ranar wajen wayar da kan dalibai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalolin da ake fama da su sakamakon gazawar gwamnatin tarayya.

Yajin aikin ASUU saboda rashin cika alkawarin gwamnatin tarayya
Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa, ASUU ta bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun shugabanta, Haruna Musa, da sakatarenta, Yusuf Madugu, da suka bayyanawa manema labarai a Kano a ranar Juma’a 4 ga watan Fabrairu.

A 2020, ASUU ta shiga yajin aikin na kusan watanni 10 bayan da ta dakatar da ayyukan masana'antu a watan Disamban 2021, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Sai dai kuma tun daga wancan lokacin kungiyar ke zargin gwamnati da rashin cika alkawuran da ta dauka, don haka ake kara fargabar sake tsundumawa sabon yajin aiki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Gobara ta lakume mahakar danyen mai ta Shebah a yankin Neja Delta

FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

A baya, ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce ma'aikatar kudi da tsare-tsare ta tarayya za ta fara rabon kudade ga jami'o'i a ranar Laraba, rahoton Premium Times.

Ministan ya ce gwamnati na da tabbacin cewa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ba za ta tafi yajin aikin da ta shirya zuwa ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin 'Politics Today' na Channels TV a ranar Talata, 16 ga watan Nuwamba.

A ranar Litinin, Victor Osodeke, shugaban kungiyar ASUU ya ce za su tafi wani yajin aikin idan gwamnati ta ci gaba da saba yarjejeniyar 2020.

Kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar bayan ta janye yajin aikin watanni tara da ta shiga a watan Disamban 2020.

Mista Ngige ya ce gwamnati ta rigada ta cika alkawarin biyan kason farko a watan Janairu kuma tana shirin biyan wasu alawus-alawus na Naira biliyan 22.72.

Kara karanta wannan

Rudani: Saura kwanaki APC ta yi taron gangaminta na kasa, INEC bata sani ba

ASUU za su tsunduma yajin aiki

A wani labarin, Kungiyar Malaman jami'a a Najeriya ASUU a ranar Juma'a ta bayyana cewa zata shiga yajin aiki saboda gwamnatn Buhari bata shirya cika alkawuran da tayi mata ba.

ASUU ta siffanta abinda Gwamnatin tarayya ke yi matsayin abin kunya musamman kan na'urar IPPIS duk da hujjoji daga ofishin Odito-Janar cewa ba tada inganci.

A jawabin da ASUU ta saki ranar Juma'a, ta bayyana yadda Gwamnati ta ki aiwatar da shawarin da aka yanke a zaman ganawa daban-daban don inganta Ilimi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel