Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU

Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU

  • Malaman jami'o'in Najeriya sun bayyana cewa su fa sun cire kauna da gwamnatin Shugaba Buhari
  • ASUU ta saki jawabin mai zafi cewa daga yanzu ba zasu sake zama da gwamnati kan wani sulhu ba
  • Sun siffanta Shugaba Buhari a matsayin maras cika alkawarin da ya dauka

Abuja - Kungiyar Malaman jami'a a Najeriya ASUU a ranar Juma'a ta bayyana cewa zata shiga yajin aiki saboda gwamnatn Buhari bata shirya cika alkawuran da tayi mata ba.

ASUU ta siffanta abinda Gwamnatin tarayya ke yi matsayin abin kunya musamman kan na'urar IPPIS duk da hujjoji daga ofishin Odito-Janar cewa ba tada inganci.

A jawabin da ASUU ta saki ranar Juma'a, ta bayyana yadda Gwamnati ta ki aiwatar da shawarin da aka yanke a zaman ganawa daban-daban don inganta Ilimi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ka tabbatar ka tsare Kaduna kafin ka yi ritaya, Shehu Sani ga Buhari

Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU
Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU Hoto: @asuu
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kungiyar ASUU, shiyar jami'ar Jos, Dr Lazarus Maigoro, ya rattafa hannu kan jawabin.

Malaman suka ce:

"Mun gaji da yaudararsu kuma LOKACI YAYI DA ZAMU DAU MATAKI. Muna sanar da yan Najeriya cewa mun gaji da zaman tattaunawa maras amfani da Ministan kwadago, Shugaban NUC, hukumar Albashi, NITDA da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa."
"Idan suna son mu sauraresu, su aiwatar dukkan alkawuran da suka yi."
"A yanzu dai, mun yanke shawaran shiga yajin aiki har zuwa lokacin da gwamnati zata nuna gaskiya kuma a cika alkaruwanmu. Mun gaji da jeka ka dawo."

ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, a jiya ta sanar da gwamnatin tarayya cewa ba za ta samu kwanciyar hankali ba har sai ta sasanta da su kan halin da ilimin jami'o'i ke ciki.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya kaddamar da shirin rage haihuwa a Nigeria

A wata zantawa da manema labarai a Awka, shugaban ASUU na jami'ar Nnamdi Azikiwe, Comrade Stephen Ofoaror ya ce ya gane yadda ake neman barazana ga zaman lafiyan kasar.

Vanguard ta ruwaito cewa, inda ya ja kunne a kan bakar guguwar da ta taso sanadiyyar gazawa wurin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka na girmama yarjejeniyar da ta yi da ASUU a ranar 23 ga watan Disamba, 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel