Rudani: Saura kwanaki APC ta yi taron gangaminta na kasa, INEC bata sani ba

Rudani: Saura kwanaki APC ta yi taron gangaminta na kasa, INEC bata sani ba

  • Ya zuwa yanzu, jam'iyyar APC bata tuntubi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ba game da taron gangamin APC
  • Wannan na zuwa ne daga wani jami'in hukumar ta INEC yayin da majiya ta tuntube shi kan ko jam'iyyar ta tuntubi INEC
  • Ko da yake jam'iyyar tana da akalla kwanaki uku don sanarwa INEC, ba a san ko hakan zai faru ba nan da 5 ga wata

FCT, Abuja - Saura kwanaki uku a yi taron gangamin APC, amma har yanzu jami'yyar bata sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ba game da taron da za a yi a ranar 26 ga Fabrairu, 2021 ba.

Kwamishinan wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri'u na INEC, Mista Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Punch jiya Talata.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano, Rimin-Gado, ya koma PDP

Taron gangamin APC ba tare da sanin INEC ba
Rudani: Saura kwanaki APC ta yi taron gangaminta na kasa, INEC bata sani ba | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Okoye ya ce:

"Ba a sanar da hukumar ba game da wani taron gangami."

Dokar zabe ta umurci dukkan jam’iyyun siyasa da su sanar da INEC duk wani taron da aka shirya gudanarwa akalla kwanaki 21 gabanin taron.

Yayin da ake sa ran za a gudanar da taron gangamin jam’iyyar a ranar 26 ga watan Fabrairu, jam’iyyar APC tana da sauran kwanaki akalla biyar; zuwa ranar 5 ga watan Fabrairu don sanar da INEC.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa jam’iyyar mai mulki ba ta yi hakan ba.

Kokarin samun martani daga jam’iyyar ya ci tura domin sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe, bai mayar da martani ga sako da aka tura masa a yammacin ranar Talata ba.

Kwamitin zaman lafiya karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka kafa domin sasanta bangarorin da ke rikici da juna a sama da jihohi 13, a yayin mika rahotonsa na wucin gadi a ranar Litinin din da ta gabata, ya nemi a kara masa tsawon mako guda domin kammala aikinsa.

Kara karanta wannan

Dan takara a 2023: Gwamnan APC ya ce Buhari ne zai zabi yankin da zai kawo dan takara

Sai dai, rahoton da Tribune ta fitar ya bayyana cewa, jam'iyyar ta gama tsara komai, ciki har da shirin kai wa INEC takardar sanarwar gudanar taron na gangami.

Jam’iyyar dai ta sha fama da rikici a jihohi da dama da suka hada da Osun, Ogun, Kwara, Zamfara, Delta, Bauchi, Akwa Ibom, Oyo, Kaduna, Ribas da Benue inda aka samu bangarori bayan taron gangamin jihohi.

A baya-bayan nan ma wani rikici ya barke a jihar Kebbi a tsagi daban-daban na jam'iyyar ta APC.

Hadimin gwamnan Arewa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi murabus

A wani labarin, rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ya dauki wani sabon salo ranar Laraba da daddare yayin da manyan jiga-jigan jam'iyya suka yi murabus.

The Nation ta rahoto cewa wadanda suka yi murabus daga APC din sun hada da, tsohon kwamishinan lafiya, Dakta Ahmed Gana, mai baiwa gwamna shawara, Dijjatu Bappa, da babban jigo Jamil Isyaka Gwamna.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta shiga matsi, gwamnonin kudu 3 sun ce ba ruwansu da takarar Atiku

Murabus da ficewa daga APC na Bappa da kuma Gwamna ya biyo bayan sauya shekar Dakta Ahmed Gana zuwa jam'iyyar PDP mai hamayya kwana biyu da suka shude.

Asali: Legit.ng

Online view pixel