Innalillahi: Gobara ta lakume mahakar danyen mai ta Shebah a yankin Neja Delta

Innalillahi: Gobara ta lakume mahakar danyen mai ta Shebah a yankin Neja Delta

  • Wata mummunar gobara ta tashi a wani katafaren kamfanin mai da iskar gas a yankin Neja Delta
  • Wannan na zuwa ne daga wata sanarwa da hukumomin kamfanin suka fitar, inda suka bayyana yadda lamarin ya faru
  • Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, majiyarmu ta ce ba a samu rasa rai ba, amma gobarar ta yi barna

Hukumar gudanarwar Shebah Exploration & Production Company Ltd (SEPCOL) ta sanar da aukuwar wata gobara da ta lakume mahakar mai da iskar gas da ke gabar teku a yankin Neja Delta.

A wata sanarwa da babban jami’in kamfanin, Ikemefuna Okafor ya fitar, ya ce ma’aikatan kamfanin 10 ne ke aiki a lokacin da lamarin ya faru, duk da cewa har zuwa lokacin hada rahoton nan ba a samu asarar rai ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

Kamfanin iskar gas
Innalillahi: Gobara ta lakume wani katafaren kamfanin mai da iskar gas | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Kamfanin ya ce an fara binciken musabbabin tashin gobarar, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

A cewar sanarwar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Hukumar Shebah Exploration & Production Company Ltd (SEPCOL) tana sanar da aukuwar mumunan gobara da ta lakume mahakarmu ta bakin teku, FPSO Trinity Spirit dake Ukpokiti Terminal, sakamakon fashewar wani abu da sanyin safiyar Laraba, 2 ga watan Fabrairu 2022.
“A halin yanzu ana kan binciken musabbabin fashewar abin kuma muna aiki tare da bangarorin da suka dace don shawo kan lamarin."

Yayin da hukumar ke bayyana halin da ake ciki da kuma yiyuwar raunuka da asarar rayuka, sanarwar ta kara da cewa:

“A halin yanzu ba a samu rahoton asarar rayuka ba, amma za mu iya tabbatar da cewa akwai ma’aikatan mahakar goma a wurin kafin faruwar lamarin kuma muna aiki wajen gudanar da bincike kan lafiyarsu da tsaronsu.

Kara karanta wannan

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

“Mun yaba da taimakon da kungiyar Clean Nigeria Associates, da tawagar Chevron da ke aiki a cibiyar Escravos da ke kusa, da masu ruwa da tsaki na al’umma da kuma masunta, wadanda suka taimaka sosai tun lokacin da lamarin ya faru.

Sanarwar ta kuma kara da cewa:

"Mun sanar da dukkan hukumomin da abin ya shafa, kuma muna kira ga jama'a da su nisanta kansu daga yankin yayin da tawagarmu ta kula da rikicin ke ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da duk masu ruwa da tsaki sabbin bayanai yayin da bincike ya fara."

Wani rahoton da TheCable ta fitar ya bayyana cewa, shaidu sun ce ana fargabar akalla mutane 10 da ke aiki a mahakar ta Shebah.

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wani katafaren gidan mai

A wani labarin, shahararren gidan man da ke garin Ibadan a jihar Oyo, SAO, dake unguwar Falana, Challenge, Ibadan, a ranar Talata da yamma ya kama da wuta, Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Gobarar wadda ta tashi da tsakar rana ta tashi ne da wata tanka da aka ajiye a harabar gidan man, lamarin da ya yi sanadiyar konewar sassan tashar da dama.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an ga jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Oyo sun isa wurin da lamarin ya faru kuma a halin yanzu suna ta faman kashe gobarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel