Mutane 7 sun jikkata yayin zaben kungiyar ‘yan dako a Taraba

Mutane 7 sun jikkata yayin zaben kungiyar ‘yan dako a Taraba

  • Zaben shugabannin kungiyar 'yan dako a kauyen Sabongida da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba ya bar baya da kura
  • Mutane 7 sun jikkata sakamakon rikicin da ya barke bayan an kammala zaben
  • An tattaro cewa tsohon shugaban kungiyar ya sha kaye a zaben inda shi kuma ya nuna adawa kan haka har ya yi zanga-zanga a gaban shugaban karamar hukumar Gassol

Taraba - Mutane bakwai ne suka jikkata bayan wani sabani da ya afku kan zaben shugabannin kungiyar 'yan dako a kauyen Sabongida da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba a ranar Laraba.

Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya fara ne a karshen makon da ya gabata bayan kungiyar ta gudanar da zabe domin samar da sabbin shugabanninta na shekaru biyu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

Wani idon shaida, Nuhu Sabongida, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana kuma mutane da dama sun yarda cewar an yi shi cikin gaskiya da amana.

Mutane 7 sun jikkata yayin zaben kungiyar ‘yan dako a Taraba
Mutane 7 sun jikkata yayin zaben kungiyar ‘yan dako a Taraba Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya ce Mallam Murtala Muhammed ne ya zama sabon shugaban tare da sauran jami'ai 11 bayan ya kayar da shugaba mai ci, Yakubu Saleh.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar The Sun ta rahoto cewar bayan kayen da ya sha, sai tsohon shugaban Saleh ya je wajen shugaban karamar hukumar, Alhaji Musa Abdullahi Chul, don yin zanga-zanga.

An tattaro cewa a ranar Talata shugaban karamar hukumar ya umurci shugaban yan sandan Gassol da wasu jami'an kungiyar da su raka Saleh sannan su nada shi ya ci gaba a matsayin shugaban kungiyar.

Nuhu ya ce:

"A kokarin tursasa tsohon shugaban kan kungiyar ne rikici ya fara tsakanin kungiyoyin hamayya."

Wata majiya ta ci gaba da cewa, an samu tashin hankali a kauyen Sabongida a ranar Talata biyo bayan takun-saka tsakanin kungiyoyin biyu, wanda ya yi sanadiyar jikkata mutane bakwai.

Kara karanta wannan

2023: Kungiya ta bawa Osinbajo wa'adin kwanaki 30 ya fito ya nemi kujerar Buhari

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Shugaban Kungiyar cigaban Sabongida, Alhaji Isiaka Adamu ya dora alhakin rikicin a kan shugaban karamar hukumar Gasol kan kokarin da ya yi na tursasa tsohon shugaban.

Shugaban karamar hukumar na so tsohon shugaban ya ci gaba saboda ra'ayin siyasarsa amma mutanen basa son sa kuma cewa wannan ne yasa suka zabi Abubakar.

"Kamar yadda kuke gani, akwai fargaba lokacin da mutane suka ki cewa ya ci gaba da shirin rantsar da tsohon shugaban da aka kayar a zaben."

Shugaban kungiyar ci gaban sabon gidan ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su saita shugaban Gasol domin guje ma ci gaba da karya doka da oda a yankin.

Da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Taraba, DSP Abdullahi Usman ya ce bai riga ya samu jawabi daga hedkwatar rundunar da ke Gasol ba.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Mu ba jam'iyyar siyasa bace: ACF ta gargadi mambobinta wajen marawa dan takara baya

"Zan yi karin bayani da zarar mun samu cikakkun bayanai daga Gassol."

Da yake martani kan zargin, shugaban karamar hukumar Gassol, Alhaji Musa Abdullahi Chul ya musanta tursasa wani dan takara a kan kungiyar.

A cewarsa, Saleh Abubakar ya rubutawa karamar hukumar wasika inda ya sanar da majalisar cewa za su gudanar da zabensu inda aka tura jami’an hukumar kwadago don sanya ido kan zaben, inda ya kara da cewa an zabi shugaban da kuri’u mafi rinjaye.

Chul ya ce:

"Zaben ya kasance bisa yarjejeniyar da suka yi kuma tun da mafi rinjaye sun zabi Saleh Abubakar sai muka yi aiki da hakan kuma muka rantsar da shi."

A wani labarin, wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya, a birnin tarayya Abuja sun kama Mu'azu Magaji, tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano.

BBC Hausa ta rahoto cewa lauyansa da iyalansa sun tabbatar da kama tsohon kwamishinan a daren ranar Alhamis, inda suka ce an kama shi ne yayin da ya ke hanyar komawa masaukinsa.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

Barista Garzali Datti Ahmad, lauyansa ya fada wa BBC Hausa cewa suna zargin akwai hannun gwamnatin Jihar Kano a kamen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel