Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige

  • An samu karin haske a kan Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar da ake zargi da kashe dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar
  • Sabbin bayanai sun nuna cewa an sallami Tanko ne daga tsohuwar makarantar da ya karantar shekaru uku da suka gabata saboda zarginsa da wawure kudade
  • Hakazalika wani mazaunin yankin ya ce Tanko yana da wuyar sha'ani ta bangaren zamantakewa da mu'amala da mutane

Kano - Daily Trust ta ce karin bayanai sun bayyana kan Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar Noble Kids Academy, Kwanar Dakata da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Labarin Tanko dai ya karade ko'ina a fadin kasar bayan an kama shi kan laifin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar, wata daliba mai shekaru 5 a makarantarsa.

Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige
Mazauna Kano: Dalilin da yasa aka kori makashin Hanifa daga makarantar da ya koyar shekaru 3 da suka shige Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wani mazaunin karamar hukumar Nasarawa ya bayyana cewa an sallami Tanko ne daga wata makarantar kudi, Ete Inoh International School, a Tudun Wada, inda ya karantar sannan ya yi aiki a matsayin shugaba bisa zargin karkatar da kudade, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

Wani Usman Nuhu ya sanar da jaridar cewa Tanko ya koma Tudun Murtala bayan an sallame shi daga makarantar.

Ya kara da cewar an sasanta lamarin ne a daya daga cikin ofishin yan sanda da ke yankin.

Ya ce:

"Bayan an sallame shi daga makarantar ta farko inda ya yi aiki a matsayin shugaba kan zargin wawure kudade, sai ya koma Tudun Murtala da zama inda ya kafa makaranta, North West.
"Yayin da kasuwanci ya habbaka sai ya yi hayar wani gida a Kwanar Dakata a Yankaba sannan ya sake kafa wata makaranta mai suna Nobel Kids wanda daga nan ne aka sace yarinyar."

Ya kara da cewar Tanko ya bar makarantar North West a karkashin kulawar matarsa sannan ya mayar da hankali kan wannan sabuwar a lokacin.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: An kamo matar makashin Hanifa, an kai ta kotu, amma ta musanta komai

Mazaunin yankin ya ce shugaban makarantar da ke fuskantar shari'a a yanzu yana da matsala wajen zamantakewa da yin mu'amala da mutane.

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

A gefe guda, mun kawo cewa Minstan ilimi na kasa, Mallam Adamu Adamu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano kan matakan da ta dauka domin magance lamarin mutuwar Hanifa Abubakar, yar shekaru 5 da malaminta ya kashe ta.

Adamu wanda ya yi magana ta hannun daraktan labarai kuma jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Mista Ben Goong, a Abuja, ya yi Allah wadai da kisan Hanifa da malaminta, Abdulmalik Tanko ya yi bayan ya sace ta.

Ministan ya kuma ce yana sanya idanu sosai kan ci gaban domin tabbatar da ganin cewa an hukunta wanda ake zargin, Pulse.ng ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel