Aika-aika: Mazauna sun dauki doka a hannu, sun kone 'yan fashi da makami kurmus

Aika-aika: Mazauna sun dauki doka a hannu, sun kone 'yan fashi da makami kurmus

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an samu yunkurin fashi a wani yankin jihar Imo daga wasu 'yan fashi
  • Rahoton ya ce tuni an kama wadanda ake zargi, inda aka kone biyu daga cikinsu kurmus nan take a yankin
  • An ce wadanda ake zargin mambobin wata tawagar 'yan fashi ne da suka addabi jama'a a yankunan garin

Jiha Imo - Rahoton The Cable na cewa mazauna sun kone wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a kauyen Eziama Obaire da ke karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo.

Legit.ng Hausa ta tattaro daga majiyar cewa, wata tawagar 'yan banga a Eziama Obaire, a ranar Alhamis, ta kama wasu da ake zargin ‘yan fashi ne guda hudu bisa zargin yunkurin sace babura a yankin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sojoji sun kame 'yan daba cikin mota gabanin zaben gwamnan Ekiti

Mazauna sun kone 'yan fashi a Imo
Aika-aika: Mazauna sun dauki doka a hannu, sun kone 'yan fashi kurmus | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya a unguwar ta shaida cewa wasu mazauna garin sun far wa mutanen hudu ne bayan da kungiyar ‘yan banga ta kama su.

Daga karshe dai an kona biyu daga cikin wadanda ake zargin ‘yan fashi ne, yayin da sauran biyun kuma aka ce sun tsere da raunuka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyar:

“Mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami sun fito ne daga titin Okwudor ta hanyar Nkume zuwa Amucha, inda suka afka wa wadanda abin ya shafa a mahadar titin Nkume ta hanyar Mgbabano-Umuaka, Eziama Obaire a karamar hukumar Nkwerre ta Imo.
“‘Yan banga a yankin sun far wa ‘yan fashin tare da kama su.”

Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun ‘yan sandan Imo, Michael Abattam, ya ce har yanzu ba a sanar da hukumar 'yan sanda faruwar lamarin ba.

Kara karanta wannan

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Ya ce:

"Zan tuntubi jami'in 'yan sanda da ke kula da yankin domin sanin hakikanin abin da ya faru."

An ce mazauna yankin sun samu karuwar ayyukan ta'addanci da barna a ‘yan kwanakin nan.

Wani shaidan gani da ido, Chikezie Nwadike ya shaidawa Daily Post cewa ‘yan fashin biyu wadanda ‘ya’yan wata tawagar 'yan ta'adda ne da suka yi kaurin suna a yankun.

Ya ce sun yi amfani da babura biyu wajen gudanar da barnarsu, sun kuma kusa yi wa wani dan acaba fashi kafin ya yi sa’a aka far wa 'yan fashin.

'Yan bindiga sun yi wa motar banki fashi

A jihar Delta kuwa, wasu 'yan fashi da makami dauke da bindigu sun farmaki motar dakon kudi ta wani Banki da har yanzun ba'a gano ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun samu nasarar fasa motar, kuma sun yi awon gaba da adadi mai yawa na kudi a kan hanyar Otor-Owhe, karamar hukumar Isoko North, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kone gine-gine 110 a Chibok, Zulum ya je ziyarar jaje

Yan fashin sun bude wa motar wuta ba kakkauta wa har sai da Harsasan bindiga suka fasa wawukeken rami a sashin motar dake dauke da kuɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel