Da dumi-dumi: Sojoji sun kame 'yan daba cikin mota gabanin zaben gwamnan Ekiti

Da dumi-dumi: Sojoji sun kame 'yan daba cikin mota gabanin zaben gwamnan Ekiti

  • Sojojin Najeriya sun samu nasarar kame wasu 'yan daba da ake zargin an tura su jihar Ekiti don tada tarzoma
  • Sojojin sun kama su da muggan makamai, wanda a har da adduna, sanduna, layu da sauran kayan aikata laifi
  • Rahotanni daga majiyoyi sun ce, ana kyautata zaton za su ta da hankali ne a wurin zaben fidda gwani da za a yi a Ekiti

Jihar Osun - A safiyar yau Laraba ne sojojin Najeriya suka kama wasu 'yan kungiyar sufuri ta NURTW ta Oyo dauke da makamai a mahadar Ita Awure/Efon a jihar Osun.

SaharaReporters ta samu labarin cewa an kama su ne da misalin karfe uku na safe.

Rahotanni sun ce ‘yan daban sun nufi Ekiti ne, domin kawo cikas ga zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa a yau.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Sojoji sun gano wata kasuwa da mafakar ISWAP, sun kone su kurmus

An kama 'yan daba a osun
Da dumi-dumi: An kame 'yan daba makare da mota suna dauke da muggan makamai | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

An tattaro cewa an hada 'yan daban ne ne daga jihar Oyo domin hana fitowar wani dan takarar gwamna a zaben 2022.

An kama su da bindigogi, adduna, layu da sauransu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, ya tabbatar da cewa, an kama wadanda ake zargin ne aa motocin bas guda biyar masu daukar fasinjoji 18, kuma suna kan hanyar Ijebu-Ijesa-Ita Ore, inda sojoji suka kama su da yammacin ranar Talata.

Abutu ya ce an kama wadanda ake zargin ne da muggan makamai na gida da aka kera da bindigu, inji rahoton Daily Trust.

Kakakin ‘yan sandan ya ba da tabbacin cewa jami’an hukumar za su yi cikakken bincike game da lamarin tare da hukunta wadanda ke da laifi a cikinsu.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Rikici ya barke a Legas, gwamnati ta dakatar da kungiyar sufuri ta NURTW

A wani labarin, a ranar Talata ne gwamnatin jihar Legas ta dakatar da ayyukan kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW) a Eyin Eyo da ke Church Street da gadar Idumota a tsibirin Legas, Vanguard ta ruwaito.

Dakatarwar da ba a bayyana lokacin dage ta ba ta zama dole ne bayan tashin hankali da aka samu a yankunan.

Mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin sufuri Oluwatoyin Fayinka ne ya sanar da dakatar da aikin kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel