Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika

  • Yan sanda a jihar Ribas sun samu nasarar kama wani matashi da ake zargin ya kashe budurwan sa kuma ya gudu
  • Rahoto ya bayyana cewa an tsinci gawar budurwar tasa a gidan da suke zaune kwanaki da dama bayan ya ɓace an daina ganin sa a yankin
  • Kwamishinan yan sandan jihar ya ba da umarnin tsananta bincike kan wanda ake zargin domin ya faɗi abin da ya kashe matar

Rivers - Hukumar yan sanda reshen jihar Rivers ta kama wani matashi, Kelechi, wanda aka gano gawar masoyiyarsa a gidan da suke zaune.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an tsinci gawar budurwan ne a gidansu dake layin Woke a kan hanyar Chirubim, Diobu, a Patakwal.

Kakakin hukumar yan sandan, SP Grace Iringe-Koko, ranar Litinin, tace yanzun haka ana tsare da mutumin a sashin binciken manyan ƙaifuka (SCID).

Kara karanta wannan

Hotuna: Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba

Jihar Ribas
Dubun wani matashin saurayi da ake zargi da kashe budurwarsa ya cika Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Iringe-Koko ta bayyana cewa kwamishinan yan sanda na jihar Ribas, Friday Eboka, ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan wanda ake zargin.

A cewar kwamishinan mutumin ya san yadda aka yi budurwarsa, Ifeoma Uzoigwe, ta rasa rayuwarta da kuma abin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Meya faru budurwar ta mutu?

Tun a watan Disamba, 2021, aka gano gawar matar yayin da ta fara ruɓewa kuma warin ta ya mamaye makotan gidajen dake layin.

Wata majya daga hukumar yan sanda ta shaida wa manema labarai cewa Kelechi, ya gudu daga Anguwar baki ɗaya tun kafin mutane su gano gawar matar.

Mai kula da yankin, Chinonye Anurum, ya ce yan sandan ofishin Nkpolu sun kama wanda ake zargin ne bisa taimakon iyalansa, waɗan da suka gano inda ya ɓoye bayan wata ɗaya da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bindige 'yan sanda har Lahira, sun yi awon gaba da babban ɗan kasuwa a Jigawa

Ya ce:

"Yan sanda sun miƙa Kelechi ga sashin SCIID, kuma an sake kira na domin ba da rahoto kan lamarin bayan na farko da na rubuta a watan Disamba."

A wani labarin kuma Matar shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta goyi bayan kashe waɗan da suka ci zalin Hanifa a bainar jama'a

Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari , ta shiga jerin yan Najeriya dake kiran a ɗauki tsattsauran mataki kan makasan Hanifa Abubakar.

Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta kan hukuncin kashe mutumin da ya kashe Hanifa a bainar jama'a domin hakan ya zama darasi ga yan baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel