An kama tsohuwa yar shekara 80 da wata mata suna yunkurin garkuwa da mutane

An kama tsohuwa yar shekara 80 da wata mata suna yunkurin garkuwa da mutane

  • Kotu ta umarci a cigaba da tsare wasu mata biyu da ake zargi da yunkurin garkuwa da mutane a gidan gyaran hali na jihar Oyo
  • Yan sanda sun gurfanar da matan, dattijuwa yar shekara 80 da wata mata da zargin amfani da mota wajen sace mutane a Ibadan
  • Alkalin kotun ya yi watsi da bukatar waɗan da ake zargi yayin zaman, ya kuma umarci a cigaba da tsare su har zuwa zama na gaba

Ibadan - Wata kotun majistire a Iyaganku, Ibadan, ta bada umarnin a tsare wata tsohuwa yar shekara 80, Oluyemi Ajani, da Dasola Orolade, yar shekara 50, a gidan gyaran hali na jihar Oyo.

Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta ba da wannan umarnin ne ranar Laraba bisa zargin matan biyu da yunkurin yin garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

Hukumar yan sanda ta jihar ta gurfanar da matan biyu ne bisa tuhumar cin amana, yunkurin yin garkuwa da kuma barazana.

Jahar Oyo
An kama tsohuwa yar shekara 80 da wata mata suna yunkurin garkuwa da mutane Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Alkalin kotun, mai shari'a Emmanuel Idowu, ya yi watsi da bukatar waɗan da ake zargi saboda rashin ƙarfin ikon kotun kan lamarin.

Sai dai ya umarci hukumar yan sanda ta kai kundin tuhumar da ake wa mutanen ga hukumar zartar da hukunci (DPP).

Kazalika, Alkalin, bayan sauraron kowane ɓangare ya ɗage zaman shari'ar har zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, 2022.

Yadda suka yi yunkurin garkuwa

Tun da farko, mai gabatar da ƙara a ɓangaren hukumar yan sanda, Sajan Iyabo Oladoyin, ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin sun yi yunkurin sace mutane a wata motar Toyota.

A jawabin sa ga kotu, yace:

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

"A ranar 3 ga watan Nuwamba, 2021, matar da yan tawagarta sun yi yukurin garkuwa da mutane a Alakia, kan hanyar Wema dake Ibadan da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
"Sun yi amfani da wata motar Toyota Corolla mai lambar rijista APP 695 GK wajen aikata mummunan nufin su."

A wani labarin na daban kuma Wata mata ta ɗauki cikin surukinta, ta haifi jikanta saboda ɗiyarta ta gaza samun juna biyu

Maree Arnold mai shekara 54 a duniya ta haifi diyarta ba tare da mahaifa ba, sakamakon haka ba ta iya ɗaukar juna biyu.

Matar ta kuma amince ta zama mahaifiyar kwayayen ɗiyarta da na mijinta, kuma ta haifi jikanta cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel