Ruɗani: Wata mata ta ɗauki cikin surukinta, ta haifi jikanta saboda ɗiyarta ta gaza samun juna biyu

Ruɗani: Wata mata ta ɗauki cikin surukinta, ta haifi jikanta saboda ɗiyarta ta gaza samun juna biyu

  • Maree Arnold mai shekara 54 a duniya ta haifi diyarta ba tare da mahaifa ba, sakamakon haka ba ta iya ɗaukar juna biyu
  • Matar ta kuma amince ta zama mahaifiyar kwayayen ɗiyarta da na mijinta, kuma ta haifi jikanta cikin koshin lafiya
  • Arnold daga ƙasar Australia, ta ce zata sake maimaita abin da ta yi, a ɗaya ɓangaren kuma ɗiyarta ta yaba wa rashin son kan mahaifiyarta

Wata mata yar kimanin shekara 54 a duniya ta haifi jikanta ta hanyar ɗaukar cikin mijin ɗiyarta.

Maree Arnold, ta yi aikin ɗauka da kuma haifar ɗan kwan halittar ɗiyarta, Meagan White, yar kimanin shekara 28 a duniya.

Jaridar 7News ta rahoto cewa matashiyar yarinyar ba ta da mahaifa, kuma sakamakon haka ba za ta iya ɗaukar juna biyu ba.

Maree Arnold
Ruɗani: Wata mata ta ɗauki cikin surukinta, ta haifi jikanta saboda ɗiyarta ta gaza samun juna biyu Hoto: Maree Arnold
Asali: UGC

Bayan shafe awanni biyu ta na naƙuda, ta haifi jariri namiji, wanda aka raɗa wa suna Winston, a ranar Alhamis 13 ga watan Janairu, 2022.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Mahaifi ya ɗirka wa diyarsa ta jini ciki saboda tsabar sha'awa

"Mun isa Asibiti da misalin karfe 7:00 na safe, kuma da ƙarfe 9:00 na haifi jaririn, ban sha wata wahala ba kuma komai a shirye yake," inji matar wacce farin ciki ya baibaye ta.

Arnold, ta bayyana tsantsar farin cikin da ta shiga kasancewar ita ta haifi jikanta da kanta.

Ta haifi ɗiyarta da wata cuta da ake wa laƙabi da MRKH ((Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser), sai dai ba kasafai ake samun mata ɗauke da irin wannan cutar ba.

Kakar jaririn ta ƙara da cewa ba zata ji kunyar kasancewa mahaifiyar 'ya'yan ɗiyarta ba kuma a shirye take ta sake haka nan gaba.

"Idan na samu lokaci nan gaba, zan sake maimaita makamancin haka. Saboda lamarin ya haifar da sakamako mai kyau."

A ɗaya bangaren kuma, White ta nuna nata farin cikin, inda ta ce ta kasa yarda wai yau ta samu ɗa kuma ta zama uwa.

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

A wani labarin na daban kuma Kungiyoyin mata sama da 600 sun mamaye titunan Abuja, sun goyi bayan gwamna ya gaji Buhari a 2023

Kungiyoyin mata daban-daban sama da 600 sun gudanar da tattaki domin nuna goyon bayan su ga takarar gwamna Yahaya Bello a 2023.

Matan sun bayyana cewa Bello ya cancanci ya ɗora daga inda Buhari ya tsaya kuma yana tafiya da mata a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel