Kotu za ta yanke wa Hushpuppi hukunci a ranar Valentine a Amurka

Kotu za ta yanke wa Hushpuppi hukunci a ranar Valentine a Amurka

  • Wata kotun kasar Amurka ta ce a ranar 14 ga watan Fabrairu (ranar Valentine) ne za a yanke wa Ramon Abbas (Hushpuppi) hukunci
  • An fara kama Hushpuppi ne a Hadadiyar Daular Larabawa, UAE, tare da wasu abokansa kan zarginsu da zamba da damfara ta intanet
  • Daga bisani an mika Hushpuppi ga Amurka bayan zarginsa da damfarar mutane miliyan 1.9 kudin da ya kai Naira biliyan 168

Ofishin Babban Antoni na yankin California ta ce za a yanke wa Ramon Abbas, mazambanci na kasa da kasa da aka fi sani da Hushpuppi, hukunci a ranar masoya ta duniya wato Valentine, The Punch ta ruwaito.

A cewar BBC Pidgin, Thom Mrozek, direktan watsa labarai na kotun, ya kuma bayyana cewa ana daf da karkare shari'ar ta Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta amince a bada kwangilolin wasu tituna 16 da za su ci Naira Biliyan 64

Kotu za ta yanke wa Hushpuppi hukunci a ranar Valentine a Amurka
Amurka: Kotu ta zabi ranar Valentine domin yanke wa Hushpuppi hukunci. Hoto: Hushpuppi
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kotun ta tsayar da ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 domin yanke wa Mr Abbas hukunci," in ji shi.

Amma, mai magana da yawun kotun bai bada wani karin bayani ba dangane da tsawon shari'ar da hukuncin da za a zartar.

Hushpuppi, wanda ya yi suna saboda rayuwa irin da ta manyan yara, ya shiga hannun hukuma ne a UAE a watan Yunin 2020 tare da wasu abokan aikata laifinsa su 11 kan zargin kutsen intanet, damfara da zamban banki.

An mayar da shi Amurka don yi masa shari'a ne bayan yan sandan na UAE sun fitar da wani faifan bidiyo mai lakabin 'Fox Hunt 2' inda ake zarginsa da damfarar mutane miliyan 1.9 kudin da ya kai Naira biliyan 168.

Daga bisani 'babban yaron' ya amsa laifin karkatar da kudade, hakan na nufin ana iya yanke masa hukuncin da ya kai daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Hushpuppi ya yi ikirarin ya bawa Abba Kyari cin hanci

A watan Yulin 2021, sunan Hushpuppi ya sake karade kafafen watsa labarai a lokacin da ya yi ikirarin cewa ya bawa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan yan sanda, cin hanci don ya kama, Chibuzo, mazabanci da suke gasa.

Duk da cewa Abba Kyari ya musanta zargin, yan sandan FBI suka yi ikirarin cewa dan sandan ya hada baki da Hushpuppi domin kama Chibuzo.

2023: Za mu bi didigin inda ƴan takara suke samo kuɗi, za mu sa ido kan asusun bankin ƴan siyasa, INEC

A wani rahoton kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, INEC, ta aika da muhimmin sako ga yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabanin babban zaben shekarar 2023.

Hukumar ta sha alwashin cewa za ta saka idanu a kan 'yan siyasa da jam'iyyun siyasa domin gano inda suke samo kudade domin yakin neman zabe, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kama mutane 28, sun kwato makamai da layoyi a jihar Neja

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taro da hukumar zaben ta shirya a Abuja, ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, kuma ya ce hukumar za ta saka ido kan yadda aka hada-hadar kudade ranar zabe don dakile siyan kuri'u, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel