Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

  • Malaman makarantun firamare a Abuja sun fusata, sun tsunduma yajin aiki saboda kin biyansu hakkokinsu
  • Wannan na zuwa ne watanni kusan biyu da dage wani yajin da suka yi a shekarar da ta gabata ta 2021
  • Sun bayyana cewa, ba a bi kadunsu ba, kuma hukumomi sun fi mai da hankali kan yakin neman zabe sama da bukatunsu

Abuja - Malaman makarantun firamare da ke babban birnin tarayya Abuja, sun fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Laraba, kan wasu basussukan da ke kan wasu kananan hukumomi a yankin.

Shugaban kungiyar malamai ta kasa reshen Kubwa, Kwamared Ameh Baba, ya tabbatar wa Daily Trust shirin yajin aikin da malaman suka fara a safiyar yau.

Ya ce hakan na zuwa ne biyo bayan wata takardar da kungiyarsu ta rattaba hannu a jiya Talata 25 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

Birnin tarayya Abuja: Malamai sun shiga yajin aiki
Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Baba ya bayyana cewa mambobinsu na bin kananan hukumomin bashin kudaden albashin da na karin girma, da mafi karancin albashin da aka kara tun 2011.

Shugaban kungiyar ta NUT ya ce wani bangare na yarjejeniyar da suka yi na janye yajin aikin da suka yi a watan Nuwamba ya samo asali ne daga tsoma bakin Sanatan babban birnin tarayya, Philip Aduda, wanda ya ce za a fara biya musu bukatun nan take.

A baya dai sun dage yajin aikin ne a ranar Juma'a 3 ga watan Nuwamba, bayan shafe akalla mako guda suna yajin, inji rahoton Premium Times.

A cewarsa:

"Amma har yanzu ba su cika alkawarin ba, kuma ga dukkan alamu sun fi damuwa da taron yakin neman zabensu wanda a halin yanzu ke mamaye fadar."

Kara karanta wannan

2023: Miyetti Allah ta ce ta na bayan Tinubu, ta bayyana taimakon da ya yi mata a baya

An ruwaito cewa malaman firamare sun shiga yajin aikin kusan sau uku a bara. Yajin aikin na karshe da suka fara ya dauki tsawon makonni biyu ana yi.

Bayan likitoci da malaman makaranta, ma’aikatan kotu sun tafi yajin-aiki a Najeriya

A wani labarin, rahotanni daga Daily Trust da sauran jaridu su na tabbatar da cewa ma’aikatan shari’a sun shiga yajin-aiki, har an kai ga rufe kotu da-dama a Najeriya.

Shugaban kungiyar malaman shari’a na bangaren jihar Legas, Kehinde Shobowale Rahamon, ya bayyana abin da ya sa ma’aikatan su ka tafi yajin-aiki.

Mista Kehinde Shobowale Rahamon ya ce har yanzu doka ta 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai ba ta fara aiki ba har yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel