Kaduna: Rikici ya barke a wata unguwa bayan manoma sun datse kan makiyayi

Kaduna: Rikici ya barke a wata unguwa bayan manoma sun datse kan makiyayi

  • Rikici ya barke a wata anguwa da ke Kaduna bayan wata hayaniya ta shiga tsakanin wasu manoma da kuma wani makiyayi
  • Hakan ya sa manoman suka sare kan makiyayin kuma suka wuce da shi yayin da sauran abokan kiwon nasa suka kora shanunsa
  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi alawadai da wannan kisan wanda ya auku tsakanin iyakar karamar hukumar Kauru da Zangon Kataf

Kaduna - Wani rikici ya barke a wata anguwa da ke cikin Jihar Kaduna bayan wata hayaniya ta auku tsakanin manoma da wani makiyayi akan dabbobi sun shiga iyakar gonar su, Vanguard ta ruwaito.

Manoman sun datse kan makiyayin sannan suka dauke kan inda suka wuce da shi, hakan yasa sauran abokan kiwon nasa suka tafi da shanun sa.

Kara karanta wannan

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

Kaduna: Rikici ya barke a wata unguwa bayan manoma sun datse kan makiyayi
Rikici ya barke a Kaduna bayan manoma sun datse kan wani makiyayi. Hoto: Vanguard NG
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi alawadai da kisan wanda ya auku a iyakar karamar hukumar Kauru da Zangon Kataf kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana.

Gwamnatin ta yi wa mazauna yankin ta’aziyyar rashin da suka yi na dan uwansu da abokan arziki kuma ta bukaci su bar jami’an tsaro suyi ayyukan su bayan ganin yadda rikicin ya janyo tashin hankali a yankin.

Har yanzu ba a gano wadanda suka yi aika-aikan ba

Vanguard ta bayyana yadda jami’an tsaro suka ce har yanzu ba a gano wadanda suka halaka makiyayin ba a yankin Zaman Chawai da ke karamar hukumar Kauru.

Kamar yadda rahoton ya zo, makiyayin, Yusuf Mahmuda, wanda mazaunin yankin ne yana tsaka da kiwon sa cikin dajin da ke kusa da wasu gonaki lokacin da wasu suka kai masa farmaki bayan wata hayaniya ta shiga tsakanin su saboda wata iyakar gona.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, a wata takarda ya bayyana yadda wani rikici ya auku a kasuwar Bakin Kogi da ke karamar hukumar Kauru ana tsaka da cin kasuwar da ke kusa da iyakar garin da karamar hukumar Zangon Kataf.

Mutum daya ya rasu yayin da mutane 2 suka samu miyagun raunuka

An halaka makiyayin, Ahmad Aliyu yayin da wasu mazauna biyu, Esther Thomas da Tanko Dakar suka samu miyagun raunuka sannan aka babbaka wani abin hawa.

Rundunar Operation Safe Heaven ne ta kai dauki wurin inda ta samu nasarar raka ‘yan kasuwa da masu siyayya don gudun rikicin ya afka musu.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana takaicin sa akan harin inda ya bayyana kokarin gwamnati da jama’an tsaro na ganin sun kawo zaman lafiya da tsaro bayan kashe-kashen da ya tayar da kura a yankin.

Har yanzu jami’an tsaro suna bincike akan lamarin kuma suna iyakar kokarin gano wadanda suka yi aika-aikan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel