'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

  • Jami'an yan sandan Adamawa da taimakon mafarauta sun yi nasarar ragargazar yan fashi a mabuyarsu da ke yankin Gangtum a karamar hukumar Ganye ta jihar
  • A cikin haka, jami'an tsaron sun yi nasarar ceto wasu mutane biyu, bdullahi Buba da wata Halima Ishaku, wadanda aka yi garkuwa da su a ranar 19 ga watan Janairu
  • Sun kuma yi nasarar kashe biyu daga cikin yan fashin a yayin da ake musayar wuta, sannan sauran sun tsere da raunuka

Adamawa - Mafarauta da jami'an yan sandan jihar Adamawa sun kakkabe wasu yan fashi daga mabuyarsu a yankin Gangtum da ke karamar hukumar Ganye ta jihar.

Farmakin da suka kai mabuyar wanda ya shafe tsawon awanni da dama, ya yi sanadiyar ceto dattijo mai shekaru 60, Abdullahi Buba da wata Halima Ishaku, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa
'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar, DSP Sueliman Nguroje, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa aikin, wanda jami'an rundunar reshen Ganye da mafarauta suka gudanar a tsaunin Shiga da Niya wanda ke a kauyen Gangtum, ya haifar da sakamako mai kyau sosai.

An tattaro cewa maharan sun yi garkuwa da mutanen ne a ranar 19 ga watan Janairu 2022 sannan suka kai su mafakar, yayin da ake tattauna kudin fansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma nuna cewa an kashe biyu daga cikin maharan a yayin da ake musayar wuta, sannan sauran sun tsere da raunuka daga harbi.

Daily Post ta rahoto cewa kwamishinan yan sandan jihar, Mohammed Ahmed Barde, wanda ya jinjinawa DPO na Ganye da jami'ansa da mahara a kan kokarinsu, ya umurci sauran DPO da su kakkabe mafakar miyagu a yankunansu.

Zan sako shi idan 'yan sanda suka saki mahaifina, in ji wanda ya sace Kwamishina

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

A wani labari na daban, wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan cinikayya da kasuwanci na jihar Bayelsa, Mista Otokito Federal Oparmiola, sun tuntubi sarkin garinsa, Otuokpoti a karamar Hukumar Ogbia ta Jihar.

Wadanda suka sace Otokito, wadanda ake ganin suna gudanar da haramtacciyar masana'antar tace mai sun farmaki gidansa da ke garin a daren ranar Alhamis, sannan suka dauke shi daga dakinsa da bindiga zuwa wajen wani kwale-kwale da ke jira a bakin ruwa sannan suka tsere.

An tattaro cewa sun yi garkuwa da Otokito kan ya yi adawa da shirinsu na kafa haramtacciyar masana'antar tace mai a dajin garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel