Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

  • Yan fashi dauke da muggan makamai sun kai farmaki garin Dankade da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi
  • Maharan sun hallaka mutane da dama sannan suka yi awon gaba da wasu saboda sun ki biyan harajin da suka daura masu
  • Kakakin yan sandan jihar, Nafi’u Abubakar, ya ce an kashe sojoji biyu da dan sanda a wannan rana a garin Dankade

Kebbi - A ranar 14 ga watan Janairu, wasu gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki garin Dankade da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi.

A yayin farmakin, maharan sun kuma kashe a kalla mutane 17 sannan suka yi awon gaba da wasu da dama.

Mazauna yankin sun ki biyan harajin kariya na naira miliyan 25 da yan ta'addan suka sanya masu, wasu da suka tsallake rijiya da baya a harin suka sanar da Premium Times.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji
Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Rahoton ya kawo cewa kimanin shekaru uku kenan mazauna wannan gari ke rayuwa a karkashin ikon yan ta'adda da suka addabi Akao, wani karamin kauye a kan iyakar jihar da Zamfara.

’Yan fashin, karkashin Bello Turji, sanannen sarkin ‘yan fashi, su ne jagorori a cikin wannan yanki mara gwamnati.

A yayin farmakin, yan bindigar sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi sannan suka kona gidaje da shagunan kayan abinci lamarin da ya shafe tsawon awanni masu yawa.

Biyan harajin naira miliyan 25 ko a mutu

Yan fashin sun sanya harajin kariya na wata-wata kan garin Dankade, wanda mazauna yankin ke biya ta hannun hakiman kauyukansu, wasu majiyoyi suka sanar da jaridar.

Yan bindigar na tara miliyoyin nairori duk wata daga wannan haramtaccen haraji da suke karba, wanda da shi ne suke siyan makamai don ta'asarsu. Hakan na wakana ne tun a 2020.

Kara karanta wannan

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

A watan Disamban 2021, yan fashin kara harajin, inda suka sa kauyukan K’lanko, K’Daba, Kurgiya, Ragaam da Dankade biyan naira miliyan 5 kowannensu. Sun bukaci hakiman kauyukan da su tabbatar da biyan kudin kafin karshen shekara.

Wani mai rajjin kare hakkin dan adam wanda ya fahimci abun da ke faruwa a yankin, Bamaiye Aniko, ya sanar da cewa:

"Musamman abun da suke so wadannan kauyuka su yi shine cewa bayan biyan naira miliyan 5 kowannensu, sai su basu damar tarawa da mata da yayansu mata.
"Sannan abu na biyu, suna son daukar dabbobin mazauna kauyukan a duk lokacin da suke so. Wannan shine mummunan sharuddan da suka basu."

Sai dai kuma, tura ta kai bango, mutanen kauyen da ke cike da takaici sun yi tawaye ga sabbin dokokin.

Farmakin rana tsaka

Da misalin karfe 3:00 na rana a ranar Juma'a, 14 ga watan Janairu, yan bindigar sun bayyana daga sansaninsu na daji a Akao sannan suka tsallaka Dankade ta kogin da ke iyakar Kebbi da Zamfara.

Kara karanta wannan

Samun man fetur ya yi wahala, jama'a sun koka, sun ce za su fara zanga-zanga

Mazauna kauyukan sun tsere cikin jeji a lokacin da suka hango miyagun da bindigogi. Sai dai kuma ba kowa ne ya tsira ba. An kama wasu 14 da suka boye a wani daki, wanda a nan take yan fashin suka harbe ko yanka su, Premium Times ta kuma rahotowa daga wadanda suka tsira.

An kuma kashe wasu mutane hudu da aka tarar a wani gida, inda gaba daya aka rasa rayuka 17 a harin na tsakar rana.

Har wayau, maharan sun zuba mutane da dama da basu mutu ba a cikin ababen hawansu sannan suka yi awon gaba da su. Sai dai ba a san yawan mutanen da suka sace ba.

An tattaro cewa hakimin kauyen, Umaru Dutse, na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

An kashe sojoji biyu da dan sanda daya

Koda dai bai ce komai ba a kan yan fararen hular da aka kashe, kakakin yan sandan jihar, Nafi’u Abubakar, a cikin wata sanarwa, ya ce an kashe sojoji biyu da dan sanda a wannan rana a garin Dankade.

Kara karanta wannan

Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9

Abubakar ya ce:

“Da jin labarin farmakin, ‘yan sandan da ke sintiri sun yi tattaki zuwa kauyukan inda suka yi artabu da yan bindigar wanda ya yi sanadin rasa jami’inmu guda daya da sojoji biyu."

Yan bindiga na kwantawa da matanmu da yayanmu mata saboda rashin biyan harajin N2m – Mazauna Zamfara

A wani labarin, azauna garuruwa biyar da ke karkashin yankin Kurya Madaro a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan yan bindiga sun koma yiwa matansu da yayansu mata fyade saboda rashin biyan kudin harajin da suka daura masu.

An tattaro cewa mazauna garuruwan da abun ya shafa sun zabi tserewa don tsira daga ci gaban hare-hare bayan sun gaza biyan yan bindiga naira miliyan 2 da suka daurawa kowannensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel