Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji

  • 'Yan ta'adda sun kutsa kauyen Batagari da ke Maikujeri na karamar hukumar Rafi ta jihar Neja inda suka halaka mutum 1 tare da sace wasu 15
  • Kamar yadda mazauna kauyen suka sanar, miyagun sun bayyana a babura dauke da miyagun makamai kuma basu tsaya ba suka fara harbi
  • Hukumomi daga kauyen sun ce har yanzu ba su yi magana da gwamnati ba kuma ba su samu kiran 'yan ta'addan ba

Niger - 'Yan bindiga masu tarin yawa sun kai farmaki karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, a wannan karon sun sheke mutum 1 yayin da suka yi garkuwa da sauran mutanen kauyen guda 15, wadanda yawancin su mata ne.

Channels TV ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan kamar yadda aka bada labari sun kai farmaki kauyen Batagari a yankin Maikujeri na karamar hukumar, yayin da suka bayyana a kan babura.

Kara karanta wannan

Nasara: Soji sun bankado farmakin 'yan ta'adda, sun ceto dan siyasa da iyalinsa a Zamfara

Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji
Niger: Ƴan ta'adda sun sheƙe rai 1, sun tasa ƙeyar mutum 15 cikin daji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, sun iso kauyen ne yayin da suka yi ta harbi a iska dan su jefa firgici a zukatan mazauna kauyen.

Majiyoyi daban-daban sun bayyana yadda 'yan ta'addan bayan sun razanar, suka fara yawo daga gida zuwa gida suna bincikar kowanne lungu da sako suna kwasar muhimman kayayyakin mutane.

Hukumomi daga kauyen sun ce babu iyalan da suka samu zantawa da 'yan bindigan kuma ba su da masaniya game da inda su ka kai wadanda suka yi garkuwa da su.

Har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, lambar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ba ta shiga.

Nasara: Dakarun sojin Najeriya sun sheƙe ƴan ta'adda 49, 863 sun miƙa wuya, DHQ

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron kasa ta ce ta halaka 'yan ta'addan 49 a karkashin ayyukan sojojin ta yayin da 'yan ta'addan 863 suka mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Jihar Kebbi: Yadda 'yan bindaga suka hallaka da dama, tare da sace wasu saboda kin biyan haraji

Daraktan yada labarai, Bernard Onyeuko, ya sanar da hakan yayin bayar da bayani kan ayyukan sojojin a ranar Alhamis a Abuja, Premium Times ta ruwaito.

Onyeuko ya ce sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun halaka 'yan ta'adda 37, sun cafke 17 tare da samo miyagun makamai 117.

Asali: Legit.ng

Online view pixel