Sabon harin ta'addanci: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna

Sabon harin ta'addanci: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai hari wani sansanin sojoji da ke jihar Katsina, sun hallaka wasu jami'an tsaro
  • An kashe soja daya da jami'in hukumar NSCDC tare da kone motoci da sace abubuwa da dama a wurin
  • Yankin da lamarin ya faru yana daga cikin inda 'yan bindiga ke yawan kai hare-hare da tafka mummunan barna

Katsina - Akalla soja daya da jami’in hukumar tsaro ta NSCDC ne suka mutu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani sansanin soji da ke unguwar Shinfida a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Wata majiya ta ce nan take ‘yan bindigar suka far wa sansanin sojojin, inda suka fara harbe-harbe, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindiga sun yi mummunan barna a jihar Kastina
Innalillahi: 'Yan bindiga sun afkawa sansanin sojoji a Katsina, sun yi barna | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce ‘yan bindigar da suka mamaye sansanin da misalin karfe 10 na daren ranar Talata, sun kuma kona motocin sintiri guda biyu tare da sace wata guda da suka dauki kayan abinci da suka sace daga kauyukan da ke kewaye.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da ke gudun ceto rai su na kai farmaki yankunan Zamfara, Dan majalisa

Majiyar ta kara da cewa wadanda harin ya rutsa da su sun mutu nan take yayin da wadanda suka samu raunuka kuma ke jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyar:

“’Yan ta’addan sun kai hari a sansanin soji da ke cikin Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Shinfida a ranar Talatar da ta gabata. Nan take suka kashe soja daya da jami’in NSCDC daya tare da jikkata wasu da dama.
“Sun kai wa sansanin sojoji hari akan babura. Duk da kokarin da sojojin suka yi, ‘yan ta’adda sun kashe mutanen biyu tare da kona motocin sintiri guda biyu da kuma sace daya da kayan abinci da suka sato daga kauyukan da ke makwabtaka."

A watan Satumba, 2021, 'yan ta'addan sun yi wa dakarun Soji na musamman na Super Camp 4 kwanton bauna, an kashe jami'an soji uku yayin da wasu da dama suka samu raunuka a harin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

Yayin da hukumar NSCDC ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, ba a samu jin ta bakin DSC Muhammad Abdara, mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya.

‘Yan bindiga sun afka Malumfashi, sun halaka maza 2 sannan sun sace wata mata da yaran ta 2

A wani labarin, ‘yan bindiga sun afka garin Makurdi da ke karkashin karamar hukumar Malumfashi a cikin jihar da daren Talata, Vanguard ta ruwaito.

Sakamakon harin, mutane biyu sun rasa rayukansu sannan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wata mata da yaranta biyu.

Sun isa garin ne da yawansu don sun wuce goma kamar yadda majiyar da ta sanar da Vanguard ta shaida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel