Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari wani yankin jihar Imo, sun fille kan wani tsoho mai shekaru 65 da daddare
  • Mazauna yankin sun shaida cewa, sun wayi gari ne suka ga an rataye kan marigayin a wata bishiya a cikin wata makaranta
  • Yankin da lamarin ya faru na daga cikin yankunan da ke fama da rashin tsaro, musamman tun a shekarar da ta gabata

Jihar Imo - An fille kan wani mutum tsoho mai shekaru 65 a Ubudom Atta da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo.

Bayan fille kan mutumin mai suna Nnoruoka Onyeokwu, an nuna kan nasa a makarantar firamare da ke unguwar.

Yankin Njaba dai ya sha fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe tun shekarar da ta gabata.

Rikcin 'yan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar wani tsoho a jihar Imo
Rashin imani: Wasu 'yan bindiga sun yiwa tsoho mai shekaru 65 yankan rago | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wakilin jdaridar Daily Trust ya tattaro cewa an kai wa mamacin hari ne a gidansa da daddare inda mutanen kauyen suka farka washegari sai suka hangi kansa a rataye akan wata bishiya a harabar makaranta.

Har ila yau, da yake magana da Daily Sun, shugaban yankin ya bayyana cewa an kai wa Nnoruka Onyeokwu hari ne a cikin gidansa da daddare.

Ya zuwa yanzu, ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ba.

A bangare guda, a ranar 8 ga Disamba, 2021, an sace basaraken gargajiya na yankin mai suna Edwin Azike, aka jefar da gawarsa a tsakiyar kasuwa.

Hakan ya biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai tare da kona hedikwatar ‘yan sanda, kotun Majistare da kuma wata cibiyar lafiya a cikin yankin a cikin watan Yuni.

Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'iza

A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki wurin Jana'iza a Ezinifitte, karamar hukumar Nnewi South, jihar Anambra, inda suka tarwatsa mutanen da suka halarci wurin.

Daya daga cikin bakin da suka halarci jana'izar, wanda ya zanta da Daily Trust yace, Jana'izar ta kare babu shiri, bayan maharan sun mamaye yankin.

Mutumin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace yan bindigan sun kai harin ne bayan samun labarin wani babban mutum a yankin yana bikin birne yar uwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel