Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9

Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9

  • Yan bindiga da ke ta'asa a dajin Gando na karamar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara sun aike wasika zuwa wasu garuruwa tara
  • A wasikar, yan bindigar sun nemi mazauna yankin su biya haraji ko kuma su dandana kudarsu
  • Wata majiya a masarautar Bunun Zugu, da ke karamar hukumar Bukkuyum ta tabbatar da lamarin

Zamfara - Yan bindiga da ke ta'asa a dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum na jihar Zamafara sun aika wasika zuwa wasu garuruwa tara inda suka nemi su biya harajinsu ko kuma su fuskanci mummunan hari.

Hakan na zuwa ne yan makonni bayan kisan kiyashin da yan bindiga suka yi wa a kalla mutane 200 a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka.

A wannan harin, yan bindigar sun kona kauyuka biyar, suka kashe mazauna garin da dama sannan suka yanka gawarwakinsu.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9
Ku biya mu haraji ko ku dandana kudarku: Yan bindiga sun aika wasiku ga kauyukan Zamfara 9 Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa yan bindigar da suka kai farmaki kauyukan a kan babura sun haura 500.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An aika wasikar ne zuwa garuruwa daban-daban, kuma kowani wasika na dauke da sunan garin a sama da yawan kudin da ake so su biya. Akwai kuma lambobin waya a jikin wasikun.

Daya daga cikin wasikun ya zo kamar haka:

“Yargalma. N5,000,000. Daga Dogon Sabi na Auwali Wanzam. Ku zo a sasanta ku biya kudi ku zauna lafiya idan ba haka ba ku tashi. Ku rike wannan shine zaman lafiyar garinku."

Duka wasikun iri guda ne banbancin shine sunan gari da kuma yawan kudin da yan bindigar ke neman a biya.

Garuruwan da yawan kudin da ake so su biya

Gundumar Zugu tana da garuruwa guda biyar da aka ci tara kamar haka: Wawan Iccen Ibrahim N4,000,000, Wawan Iccen Salihu N1,000,000, Gaude N1,000,000, Galle N1,000,000 da Tungar Gebe N500,000.

Kara karanta wannan

Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su

A gundumar Gado, garuruwa biyu da aka ci tara sune Nannarki da Ruwan Kura N5,000,000 kowanne.'

Yankin Adabka na da gari daya Gangara guda daya wanda aka ci tara Naira miliyan 1.5. Gundumar Zarummai kuma tana da gari guda daya wato ‘Yar Galma N5,000,000.

Premium Times ta ce ta zanta da wata majiya a masarautar Bunun Zugu, a karamar hukumar Bukkuyum wacce ta tabbatar da cewa koda dai kauyukan tara na a fadin gundumomi hudu ne, an tura dukka wasikun zuwa Bunun Zugu ne.

Majiyar fadar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce sarkin ya tuntubi Sarkin Bukkuyum kan lamarin.

"Mai martaba yana ta tattauna batun da Hakimin gundumar da sauran shugabannin sauran gundumomin."

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

A wani labarin, a kalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu masu tarin yawa suka jigata bayan 'yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta a jihar Kaduna, TVC News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun gasa wa 'yan ISWAP ayya a hannu yayin da suka kai hari a Biu

'Yan ta'addan sun bayyana a babura inda suka tsinkayi wurin bikin da ake yi a kauyen Dikko da ke karamar hukumar Giwa ta jihar a ranar Juma'a kuma suka dinga harbe-harbe babu kakkautawa, lamarin da ya tsorata jama'a.

Mutum hudu daga cikin 'yan bikin aka halaka yayin da wasu suka jigata kuma aka mika su asibiti domin samun taimakon gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel