Gwamna ya ce jiharsa ce kan gaba wurin yawan Yahoo Boys a Najeriya

Gwamna ya ce jiharsa ce kan gaba wurin yawan Yahoo Boys a Najeriya

  • A ranar Juma’a gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ya ce Jihar ita ce tafi ko wacce yawan ‘yan damfarar yanar gizo a Najeriya
  • Ya bayyana yadda ‘yan damfarar suka shirya biki na musamman don bayar da jinjina da kyautuka ga wanda ya fi kowa iya damfara
  • Gwamnan ya ce shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan yayin wani taro da su ka yi a garin Abuja inda ya kaddamar da shirin yakar ‘yan damfarar

Jihar Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun a ranar Juma’a ya ce jihar ta fi ko wacce a Najeriya yawan ‘yan damfarar yanar gizo, wato Yahoo Boys, Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a jihar har wani taro na bayar da lambar yabo ‘yan damfarar suka yi a Abeokuta inda suka raba kyautuka ga wanda ya fi kowa kwarewa a damfara a tsakaninsu.

Gwamna ya ce jiharsa ce kan gaba wurin yawan Yahoo Boys a Najeriya
Gwamnan Jihar Ogun ya ce jiharsa ce kan gaba wurin yawan 'Yahoo Boys' a Najeriya. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Gwamnan ya yanko inda shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana hakan a wani taro da suka yi a Abuja.

Gwamnan ya kaddamar da shirin farautar ‘yan damfarar na jiharsa

Abiodun ya yi maganar ne a Arcade Ground, Oke-Mosan cikin Abeokuta yayin taron kaddamar da wani shiri na tsaro mai suna OP-MESA ranar Juma’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da ya ce Bawa ya ce “Jihar Ogun ta fi ko wacce yawan ‘yan damfarar yanar gizo.”

Gwamnan ya ce ayyukan ‘yan damfarar ya yi yawa a jihar hakan yasa suka zarce ko wacce Jiha, kuma shugaban EFCC ma yarda da wannan kiyasin.

A cewarsa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a shirye gwamnatin jihar take da ta yi yaki da damfarar kudade a Jihar, don ganin ta kawo karshen wannan mummunar dabi’ar.

Abiodun ya yi kira akan yaki akan garkuwa da mutane inda yace ba za su lamunci hakan ba.

Ya ce abin ban takaici ne

Kamar yadda ya yi jawabin:

“Ina son ganin na hana duk wani mara gaskiya zama a Jihar Ogun. Rannan mun je taro Abuja wanda shugaban EFCC ya je. Abin ban takaicin shi ne yadda ya sanar dani cewa Jihar Ogun ce ta fi ko wacce jiha yawan ‘yan damfarar yanar gizo.
“Amma na ce mishi ban yi mamakin hakan ba kasancewar a Ogun akwai makarantun ilimi kuma anan ake samun ‘yan damfara. Ya sanar da ni yadda ‘yan damfarar har taron raba kyautuka da jinjina wa junansu suka yi. Hakan yasa aka kama wasu daga cikin su.
“Don haka mun kafa hukumar da zata kawo karshen duk wasu ‘yan damfara don ba su da gurbi a Jihar mu. Muna da bangarori daban-daban amma ba ma bukatar mutane su koma bangaren damfara.”

Ya kara da shaida yadda aka kafa OP-MESA don yaki da ta’addanci a jihar inda ya tabbatar za a dauki kwararan matakai wurin kawo karshen rashin gaskiya a Jihar.

Jami’an tsaro sun ce hakan zai saukaka ayyukan su

Gwamnan ya kara da cewa kaddamar da OP-MESA zai hada da samar da ababen hawa 15 masu makamai da hanyoyin sadarwa wadanda zasu dinga zagaye wurin binciko masu laifi.

A bangaren kwamanda janar na rundunar soji 81 Division, wanda ya hada da na Legas da Jihar Ogun, Manjo Janar Lawrence Fejokwu ya yaba da kokarin gwamnan akan samar da kayan aikin da za a zakulo masu laifi.

Ya ce da taimakon gwamnan Jihar za a inganta tsaro kuma ya yalwata.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole ya ce samar da kayan aikin zai saukaka wa jami’an tsaro yin ayyukan su yadda ya dace.

Yahoo Boys sun shirya bikin karrama 'jaruman cikinsu', EFCC ta kai samame ta damke 60

A baya, kun ji cewa jami'an hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, reshen jihar Legas sun kama wasu mutane 60 da ake zargin masu damfara ne ta intanet, wato Yahoo Boys.

An kama su ne yayin da suka shirya wani biki a wani otel da ke Abeokuta domin karrama wadanda suka yi bajinta cikinsu wurin damfara, kamar yadda ta sanar a shafinta na Facebook.

Binciken da EFCC ta yi ta gano cewa bikin da suka shirya sun masa lakabi ne 'Peer Youths Awards' kamar yadda kakakin hukumar Wilson Uwujaren ya sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel