Yahoo Boys sun shirya bikin karrama 'jaruman cikinsu', EFCC ta kai samame ta damke 60

Yahoo Boys sun shirya bikin karrama 'jaruman cikinsu', EFCC ta kai samame ta damke 60

  • Jami'an hukumar EFCC sun kama wasu mutum 60 da ake zargin masu damfara ta intanet ne wato Yahoo Boys
  • An kama matasan ne yayin da suka shirya wani kwarya-kwaryan liyafa a wani otel a Abeokuta domin karrama wadanda suka fi bajinta cikinsu
  • EFCC ta ce ta kwato kayayyaki da dama a hannunsu da suka hada da motoccin alfarma, kwamfuta, wayoyin salula da wasu kayan laturoni

Ogun - Jami'an hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arziki ta'annati, EFCC, reshen jihar Legas sun kama wasu mutane 60 da ake zargin masu damfara ne ta intanet.

An kama su ne yayin da suka shirya wani biki a wani otel da ke Abeokuta domin karrama wadanda suka yi bajinta cikinsu wurin damfara, kamar yadda ta sanar a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

Yahoo Boys sun shirya bikin karrama junansu, EFCC ta kai samame ta damke 60
EFCC ta kama Yan Yahoo 60 a wani otel da ke Abeokuta. Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Binciken da EFCC ta yi ta gano cewa bikin da suka shirya sun masa lakabi ne 'Peer Youths Awards' kamar yadda kakakin hukumar Wilson Uwujaren ya sanar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kwato motoccin alfarma da wasu kayayyaki

Jami'an na EFCC sun kwato kayayyaki da dama daga hannun wadanda ake zargin.

Abubuwan da aka kwato sun hada da motoccin alfarma daban-daban, kayayakin laturoni, kwamfuta laptops da wayoyin salula.

Sanarwar da hukumar yaki da rashawar ta fitar a ranar Litinin ya ce:

"Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu nan ba da dade wa ba."

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

A wani labarin, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Kara karanta wannan

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel