Na raba wa mutane Naira miliyan 140 jajibarin zaɓen 2003 duk da na san ba zan yi nasara ba, Olusegun Osoba

Na raba wa mutane Naira miliyan 140 jajibarin zaɓen 2003 duk da na san ba zan yi nasara ba, Olusegun Osoba

  • Tsohon gwamnan Jihar Ogun, Aremo Olusegun Osoba, a ranar Laraba ya bayyana yadda aka yi masa magudin zabe a shekarar 2003 wanda ya tsaya takarar gwamna
  • Osoba ya ce ya samu labari akan yadda ake shirin murdiyar zabe inda aka shawarce shi da ya janye takarar amma duk da hakan ya tsaya a kan bakar sa
  • Ya yi wannan bayanin ne a Abeokuta, Jihar Ogun yayin wani taro na kaddamar da wani littafi da kuma shagalin cikar tsohon Sakataren watsa labaran sa, Kayode Odunaro shekaru 60

Jihar Ogun - Tsohon gwamnan Jihar Ogun Aremo Olusegun Osoba a ranar Laraba ya bayyana yadda aka yi masa murdiyar zabe lokacin da ya tsaya takarar gwamna a 2003, Daily Trust ta ruwaito.

Osoba ya ce ya samu bayanan sirri akan yadda ake shirin yin magudin zaben inda aka shawarce shi da ya dakata da takarar amma ya tsaya a kan bakar sa.

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan takara za su fuskanci matsala a 2023, ana neman gyara dokar shiga takara

Na raba wa mutane Naira miliyan 140 jajibarin zaɓen 2003 duk da na san ba zan yi nasara ba, Olusegun Osoba
Olusegun Osoba: Na raba wa mutane Naira miliyan 140 jajibarin zaɓen 2003 duk da na san za a murde min zaben. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi wannan bayanin ne a Abeokuta, Jihar Ogun yayin kaddamar da wani littafi da kuma shagalin cikar sakataren watsa labaran sa, Kayode Odunaro shekaru 60 da haihuwa a ranar Laraba.

Ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar AD a lokacin

Osoba ya tsaya takara karkashin jam’iyyar AD a lokacin shi kuma Otunba Gbenga Daniel na PDP ya kayar da shi.

A cewarsa ya san zai fadi zaben sakamakon yadda wasu jami’an tsaro suka kai masa rahoton sirri.

Amma ya ce duk da sanin cewa zai sha kaye ya raba wa jama’a N140miliyan ranar jajibarin zabe.

Ya ce ya ki zuwa kotu duk da yana da shaidun da zai gabatar

Osoba ya kara da cewa ya ki zuwa kotu akan magudin zaben duk da akwai shaidu da dama wadanda zai iya gabatarwa.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani kan kyautar da Tinubu ya bayar na N50n ga 'yan Zamfara

Kamar Daily Trust ta ruwaito ya ce:

“A zaben 2003, wanda ya faru shekaru da dama da suka shude don ban rike shi a raina ba. Na amince da sakamakon zabe duk da na san magudi aka yi.
“Na ki garzayawa kotu duk da ina da shaidun da zan iya gabatarwa kuma na share abubuwan da suka wuce. Hakan da na yi na ba mutanen Ogun damar kwatanta mulki na da na wasu.
“Babu wanda ya san zaben zai zama haka amma ni na sani saboda Farfesa Adu na FUNAAB ya gama rubuta sakamakon tun kafin a yi zaben.
“Wasu jami’an tsaro sun sanar da ni abinda ke faruwa amma ban damu ba. Na san yadda siyasa take. Har jan kunne na aka yi akan kada in tsaya takara amma na ki amsar shawarar.”

Ya ce ya san asarar kudinsa ya yi

A cewarsa ya raba naira miliyan 140 duk da ya san asarar kudi ya yi kuma idan bai raba ba cewa zasu yi ya fadi ne saboda bai saki aljihu ba.

Kara karanta wannan

Dele Momodu: Allah ne ya tanade ni na gaji Buhari a zaben 2023

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel