Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana can jihar Kaduna, ziyarar da ya kai jihar domin kaddamar da wasu ayyuka a karkashin shirin KadunaUrbanRenewal
  • Shugaban a jawabinsa a fadar Sarkin Jama’a ta Kafanchan, Alhaji Muhammadu Isa 11, ya bayyana cewa ana kokarin ganin an kare rayukan jama'a
  • Wannan yasa, Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kara amincewa da rundunar sojoji wajen yaki da rashin tsaro da ke addabar al’umma

Jihar Kaduna - A ranar Alhamis, 20 ga watan Janairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a garin Kafanchan, jihar Kaduna, ya yi gargadin cewa ba za a bari wani ya tara rundunar ‘yan daba domin tilastasu kan wasu jama’a ba.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa a fadar Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu Isa 11, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mun gyara Najeriya fiye da yadda muka same ta a 2015, Buhari ya bugi ƙirji

Sai dai Buhari ya jaddada kudirinsa na dunkule tsarin siyasar kasar domin inganta rayuwar al’umma saboda al’ummar kasar.

Jaridar Sun ta ruwaito Buhari na cewa:

"Muna yin kokarinmu don karfafa tsarin don amfanin jama'a saboda suna da mahimmanci."

Don haka, ya yi magana game da amfani da 'yan sanda da sojoji, wajen magance matsalolin tsaro, inda ya bukaci 'yan Najeriya da su bunkasa amincewa da hukumomin tsaro don gina tsarin "ba tare da hargitsi ba."

Ya aika da gargadi mai tsanani

“Babu wanda ya kamata a bar shi ya tara rundunar ‘yan daba don tilasta kansa kan mutane."

Shugaban ya yabawa gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna bisa nasarorin da ya samu wajen samar da ababen more rayuwa, bayan kaddamar da sabuwar hanyar Dan Haya, titin Katsina, da titin fadar sarki a Kafanchan.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kaduna a ranar Alhamis, inda ya tuna da yadda ya tsallake rijiya da baya da aka dasa masa bam a kusa da gadar Kawo, a lokacin da yake tafiya jihar Katsina a watan Yulin 2014.

Jaridar Vanguard ya ruwaito Buhari wanda yake a sabuwar gadar Kawo da gwamnatin El-Rufai ta gina, ya ce:

“An yi yunkurin tayar da bam a nan… akwai wata kasuwa a kusa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel