Jami'ai sun kyauta: Buhari ya yi martani kan kame mai malamin da ya sace Hanifa

Jami'ai sun kyauta: Buhari ya yi martani kan kame mai malamin da ya sace Hanifa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyayen yarinyar da aka sace aka yi mata kisan gilla a Kano
  • Jajantawarsa ta biyo bayan labarin kama wani bata-gari da ya yaudari iyayenta da ita wajen sace ta da neman fansa
  • Rahotanni sun bayyana yadda shugaban makaranta ya sace dalibarsa, ya kuma nemi kudin fansa daga iyayenta

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a da su tabbatar da tagomashi ga jami’an ‘yan sandan da suka kama makashin Hanifa Abubakar, ‘yar shekara biyar da aka kashe a Kano.

Shugaban fadi haka ne a lokacin da yake jajantawa iyayen yarinyar ‘yar makarantar, da aka gano gawarta a wani rami a Kano, bayan shafe kusan watanni biyu ana nemanta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Shugaba Buhari ya yi martani kan kashe Hanifa Abubakar
Jami'ai sun kyauta: Buhari ya yi martani kan kame mai malamin da ya sace Hanifa | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: UGC

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya yabawa aikin ‘yan sanda da jami’an sirri wajen bankado lamarin, musamman yadda aka kama malaminta da sauran abokan aikinsa.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahotanni kan yadda aka kama shugaban wata makarantar firamare da Hanifa ke zuwa da laifin yi mata kisan gilla.

A bangaren Buhari, ya jajantawa iyayen yarinyar da daukacin alummar kasar nan da suka damu da yadda lamarin ya faru.

Sai dai ya kara da cewa kwazon da jami’an tsaro suka yi na binciken gawar tare da kama wadanda ake zargin wadanda tuni suka amsa laifinsu abin yabawa ne.

Ya ce wannan nasara ce da ya kamata jama’a su kara amincewa da hukumomin tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan

Me yasa ka kashe ta: Mahaifiyar Haneefa da aka yiwa kisan gilla ta farmaki makashin 'yarta

A cewarsa:

"Lokacin da matsala irin wannan ta faru, mutane za su yi ta maganganu daban-daban game da aiwatar da doka."

Buhari ya yi addu’ar Allah ya jikan yarinyar nan da ta rasu, ya kuma bukaci iyayenta da su jure wannan rashi mai daci da yin tawakkali ga Allah.

Yadda aka sace Hanifa

An sace dalibar ne a unguwar Kawaji da ke unguwar Yankaba a cikin birnin Kano a watan Disamba a kan hanyarta ta dawowa daga makarantar Islamiyya da yamma.

Rahoton Daily Nigerian ya ce, an yaudari Hanifa ne da sunan rage mata hanya, lamarin da ya tada hankalin iyayenta, musamman kawunta Suraj.

Rahotan sace ta ya jefa jama’a cikin fargaba a fadin Kano da kasar nan baki daya, ganin yadda lamarin ya dauki hankalin jama'a a kafafen sada zumunta.

An kama wanda ya sace Hanifa, ranar Laraba, yayin da yake kokarin karbar wani bangare na kudin fansar da yace a bashi.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ba zan bari wani ya hada 'yan daba su dauki makami ba, inji Buhari

A wani labarin, shugaban makarantar Noble Kids Nursery and Primary School da ke Kano, Abdulmalik Tanko ya bayyana cewa shi ma yana da ‘ya’ya mata uku.

Tanko, wanda ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar mai shekaru biyar a watan Disamba 2021, kuma daga baya ya kashe ta, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ranar Juma’a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A baya an ruwaito yadda aka yi garkuwa da Hanifa a lokacin da take kan hanyarta ta dawo daga makarantar Islamiyya a watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel