Har da hawayen ƙarya: Mai makarantarsu Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, Kawun Hanifa

Har da hawayen ƙarya: Mai makarantarsu Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, Kawun Hanifa

  • Abdulmalik Mohammed Tanko, mai makarantar Noble Kids da ke Kwana a Kano ya je har gida don yi wa iyayen Hanifa jaje akan batar ta
  • An samu bayanai akan yadda Tanko da kansa ya amsa laifin sa gaban ‘yan sanda cewa shi ya yi garkuwa da Hanifa a watan Disamba kuma ya halaka ta
  • Kawun Hanifa, Suraj Sulaiman ya bayyana yadda Tanko ya je yana zubar da hawaye yayin da ya kai musu ziyara duk da haka ya halaka ta kuma ya amshe N6m

Jihar Kano - Abdulmalik Mohammed Tanko, mai makarantar Noble Kids da ke Kwana a Kano ya kai wa iyayen Hanifa Abubakar, dalibar makarantarsa mai shekaru 5, ziyara bayan batan ta a watan Disamba.

Daily Trust ta ruwaito yadda Tanko da kan sa ya amsa laifukan sa yayin da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano suka tasa keyar sa ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Na san zafin haihuwa: Makashin 'yar makaranta Hanifa ya bayyana adadin 'ya'yansa

Har zubar da hawayen ƙarya: Mai makarantar su Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, Kawun Hanifa
Kawun Hanifa: Mai makarantar su Hanifa ya yaudare mu yayin da ya zo jajen ɓatar ta, har kukan karya ya yi. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ya bayyana yadda ya yi garkuwa da Hanifa ya ajiye ta a cikin gidan sa daga bisani ya sa mata guba a cikin abinci. Bayan nan ya haka rami tare da birne ta a cikin harabar makarantar sa.

Har da zubar da hawayen karya ya yi

Yayin tattaunawa da wakilin Daily Nigerian, Suraj Sulaiman, kawun marigayiya Hanifa ya bayyana yadda Tanko ya zo har gida yana zubar da hawaye don jajanta wa iyayen ta.

A cewarsa:

“Ya zo yana zubar da hawaye yayin da ya kai wa iyayen ta ziyara don jaje.”

Sai da ya amshi Naira miliyan 6 a hannun iyayen ta

Sai da Tanko ya sa wa Hanifa guba ta ci a abinci sannan ya bukaci naira miliyan 6 daga hannun iyayen ta.

Kara karanta wannan

Shugaban makarantar su Hanifa ya magantu: Da gubar beran N100 na kashe ta

Bayan mahaifiyar Hanifa ta ga Tanko a hedkwatar ‘yan sanda a ranar Juma’a da safe, ta fuskance shi tana tambayarsa abinda ya sa ya yi musu haka.

'Yan bindiga sun dira a Kano, sun sace mahaifiyar ɗan majalisa

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Laraba sun sace mahaifiyar Isyaku Ali-Danja, dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa a majalisar jihar Kano.

Daily Nigerian ta rahoto cewa yan bindigan sun afka gidan mahaifiyar dan majalisar ne da ke Gezawa misalin karfe 1 na dare, suka balle kofa sannan suka yi awon gaba da ita.

Da ya ke bada labarin yadda abin ya faru, Mr Ali-Danja, wanda ya taba rike mukamin kakakin majalisa, ya ce da farko yan bindigan sun umurci mahaifiyarsa ta bude kofa amma ta ki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel