Zamu bar Najeriya a gyare fiye da yadda muka same ta lokacin muka karbi mulki, Buhari

Zamu bar Najeriya a gyare fiye da yadda muka same ta lokacin muka karbi mulki, Buhari

  • Shugaban Buhari yace gwamnatinsa ta kawo cigaba ga Najeriya fiye da lokacin da ta karbi mulki a 2015
  • Buhari, wanda ke ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar Kaduna, ya roki yan Najeriya su tantance nasarorin da gwamnatinsa ta samu
  • Sarkin Jema'a, ya roki shugaban ƙasa ya taimaka musu da sansanin sojojin sama a yankin Kafanchan

Kaduna - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata miƙa mulkin Najeriya da cigaba fiye da yadda ta ƙarba.

Ya kuma roki mutane su sa Allah a ransu yayin da zasu yi alkalanci kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu zuwa yanzu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika,, Shugaba Buhari ya bukaci yan Najeriya su masa adalci, wajen tantace alƙawurran da ya yi yayin yaƙin neman zaɓe a 2015.

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Shugaba Buhari a Kaduna
Zamu bar Najeriya a gyare fiye da yadda muka same ta lokacin muka karbi mulki, Buhari Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Shugaban ƙasan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai domin kaddamar da ayyuka a Kafanchan, Kaduna da Zaria.

Da yake jawabi a fadar mai martaba Sarkin Jema'a, Alhaji Muhammadu Isa II, a Kafanchan, Buhari ya haska maslahar da ya samar wajen karfafa tsarin siyasar ƙasar nan domin rayuwar yan Najeriya ta yi kyau.

Wace Nasara Buhari ya samu a bangaren tsaro?

Haka nan kuma, ya bayyana rawar da yan sanda, sojoji ke takawa wajen magance matsalar tsaro, amma ya roki yan Najeriya su kara dagewa wajen kafa al'ummar da zata tsira daga rikici.

Channels tv ta ruwaito Buhari yace:

"Babu wani shafaffe da mai da zamu bari ya haɗa tawagar yan daba, domin tilasta wa mutane su zaɓe shi. Ya kamata kowa ya fahimci wannan da kyau."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023

Sarki ya roki shugaba Buhari

A nasa jawabin, Sarkin Jema'a, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kafa musu sansanin rundunar sojin sama na dindindin da kuma na yan sanda.

Haka nan kuma ya bukaci gwamnatin Buhari ta sabunta layin dogo, wanda tun tale-tale aka san Kafanchan da shi.

A wani labarin na daban kuma Gwamnan Neja ya bayyana goyon bayansa ga kudirin jagoran APC, Bola Tinubu, na takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya goyi bayan kudurin jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu , ya maye gurbin shugaba Buhari a zaben 2023.

Gwamnan yace cigaba da ɗaukakar da yan Najeriya ke ganin jihar Legas ta samu, duk sakamakon tubalin da Tinubu ya gina ne a lokacin da yake gwamna, dan haka zai iya mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel