Tuna baya: Buhari ya ba da labarin yadda aka kitsa tarwatsa shi da bam a Kaduna

Tuna baya: Buhari ya ba da labarin yadda aka kitsa tarwatsa shi da bam a Kaduna

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a 2014 a gadar Kawo
  • Ya ce wasu sun yi yunkurin hallaka shi da bam a gadar, amma da ikon Allah ya samu ya tsallake dakyar
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake tare da gwamnan jihar Kaduna a kaddamar da ayyukan da El-Rufai ya yi a Kaduna

Kaduna - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Kaduna a ranar Alhamis, inda ya tuna da yadda ya tsallake rijiya da baya da aka dasa masa bam a kusa da gadar Kawo, a lokacin da yake tafiya jihar Katsina a watan Yulin 2014.

Jaridar Vanguard ya ruwaito Buhari wanda yake a sabuwar gadar Kawo da gwamnatin El-Rufai ta gina, ya ce:

Kara karanta wannan

Buhari: Saboda tsabar gyaran da El-Rufai ya yi a Kaduna, har na 'ɓace' a garin

“An yi yunkurin tayar da bam a nan… akwai wata kasuwa a kusa."
Buhari a Kaduna, ya magantu kan harin da aka kai masa
Tuna baya: Buhari ya ba da labarin yadda aka kitsa tarwatsa shi da bam a Kaduna | Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Gadar Kawo wani aiki ne na gwamnatin Kaduna, wanda ya jawo hankalin masu yawon bude ido da dama zuwa Kaduna tun bayan kammala shi.

A wani bangare na ziyarar da shugaba Buhari ya kai Kaduna, ya kaddamar da katafaren kantin siyayya da wasanni na zamani da ke Murtala Square Kaduna, inda ya kara jaddada yiwuwar zamansa a Kaduna bayan ya bar mulki.

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, shugaban ya yabawa irin hangen nesa da ci gaban gwamnatin El-Rufai, inda ya nuna cewa Kaduna ta yi kyau, bakon da ya dade bai zo zai iya bata, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Tun da farko dai, shugaba Buhari wanda ya isa Kaduna ya kasance a garin Kafanchan na Kudancin Kaduna inda ya yaba da dimbin ayyukan da ya kaddamar tare da godewa gwamnan bisa gina hanyoyi masu kyau da sauran ayyukan samar da ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Najeriya ba ta buƙatar shugaban ƙasa na ƙabilanci, Hakeem Baba-Ahmed

Ana sa ran Buhari da tawagarsa karkashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai za su kasance a Zariya a ci gaba da kaddamar da ayyukan.

A ranar Juma’a ne ake sa ran kawo karshen ziyarar da shugaban kasar ya kai Kaduna, garin da Buhari ya zauna tun bayan ritayarsa daga aikin soja.

Shugaba Buhari zai kai ziyara wani yankin jihar Kaduna ranar Alhamis mai zuwa

A wani bangare na ziyarar aiki ta kwanaki 2 a jihar Kaduna da zai fara a ranar Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Kafanchan da ke Kudancin Kaduna da sauran manyan garuruwan jihar domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka.

Buhari zai kai ziyarar kwanaki biyu a jihar Kaduna, wadda za ta fara gobe kuma za ta kare a ranar Juma'a, in ji sanarwa daga gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim, Vanguard ta ruwaito.

A cewar sanarwar:

"Shugaban zai ziyarci manyan garuruwa uku na Kaduna, Zariya da Kafanchan, za kuma a nuna mishi ayyukan tituna a fadin jihar, wanda gwamnatin gwamna Nasir El Rufa'i ta aiwatar."

Kara karanta wannan

Matsalar Tsaro: Baicin kwarewar Buhari, da Najeriya ta ruguje kurmus

Asali: Legit.ng

Online view pixel