Ni dashi duk samari ne, gayu: Shehu Sani ya zolayi Tinubu kan yawan shekarunsa

Ni dashi duk samari ne, gayu: Shehu Sani ya zolayi Tinubu kan yawan shekarunsa

  • Wani tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi rubutu a shafinsa na Twitter kan hakikanin shekarun Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Tsohon dan majalisar tarayyar ya bayyana cewa Bola Tinubu bai kai shekarun da yawancin ‘yan Najeriya ke zato ba
  • Hasali ma, cikin zolaya, tsohon Sanata Shehu Sani ya yi ikirarin cewa shi da tsohon gwamnan na jihar Legas shekarunsu daya

Kaduna - Shehu Sani ya zolayi Tinubu kan hakikanin shekarunsa a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 20 ga watan Janairu.

Tsohon dan majalisar tarayya na Kaduna ya bayyana cewa shi da shugaban na jam’iyyar APC na kasa su gayu ne.

Shehu Sani ya zolayi Tinubu
Ni dashi duk samari ne, gayu: Shehu Sani ya zolayi Tinubu kan yawan shekarunsa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sani, cikin zolaya ya kuma ce tsohon gwamnan Legas sa'an sa ne a shekare.

Ya rubuta a shafin Twitter cewa:

Kara karanta wannan

Alamar tambaya: Garba Shehu ya lallaba ya bibiyi shafin kamfen din Tinubu a Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Jagaban bai kai shekarun da kuke kwatanta shi ba, ni dashi samari 'yan gayu ne kuma sa'annin juna."

Yan Najeriya sun yi martani yayin da shekarun Tinubu ya sauka daga 79 zuwa 69 a shafin Wikipedia

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta 69 a ranar Litinin, 29 ga Maris., kamar yadda The Cable ta ruwaito.

'Yan siyasa da shugabannin Najeriya sun taya shi murna matuka a shafukan sada zumunta.

Wani mai amfani da shafin Twitter @_PLICE ne ya fara lura da bambancin shekarun bayan gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya aika sakon taya murnar zagayowar ranar haihuwa ga Tinubu a Twitter.

Mintuna kadan bayan ya ja hankali, sai wani mai amfani da shafin Twitter @oreke_lewa ya nuna cewa an gyara shekarun. Ya sauka daga 79 zuwa 69.

Kara karanta wannan

Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

'Yan Najeriya sun rarrabu a tsakaninsu kan wannene ya kasance shekarunsa na hakika. Wasu na ganin cewa ya girmi shekaru 69.

A gefe guda, makon nan ne ake bikin taya fitaccen ‘dan siyasar kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa.

Shehu Sani ya shiga rukunin wadanda su ka aika wa babban jagoran na APC mai mulki sakon taya murna a ranar Litinin, 29 ga watan Maris, 2021.

‘Dan siyasar ya ba tsohon gwamnan na jihar Legas shawarar ya dauki hayar tafinta a garin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel