Shehu Sani ya ba Jigon APC, Tinubu muhimmiyar shawara bayan ya kai shekaru 69

Shehu Sani ya ba Jigon APC, Tinubu muhimmiyar shawara bayan ya kai shekaru 69

- Shehu Sani ya taya Bola Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa

- A jiya ne babban ‘dan siyasar ya cika shekara 69 da haihuwa a Duniya

- Sanata Sani ya ba Tinubu shawarar ya dauko mai fassara masa Hausa

A makon nan ne ake bikin taya fitaccen ‘dan siyasar kudancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara 69 da haihuwa.

Shehu Sani ya shiga rukunin wadanda su ka aika wa babban jagoran na APC mai mulki sakon taya murna a ranar Litinin, 29 ga watan Maris, 2021.

‘Dan siyasar ya ba tsohon gwamnan na jihar Legas shawarar ya dauki hayar tafinta a garin Kano.

KU KARANTA: Tinubu @ 69: Buhari, Gwamnoni, Shugabannin Majalisa sun yi magana

Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019, ya fito shafinsa na Twitter, ya na cewa:

“Ina taya Asiwaju (Bola Tinubu) murnar cika shekara 69. Babban ‘dan siyasa ne kuma wanda ya yi yaki domin dawo da mulkin farar hula a Najeriya.”

"Shawara ta ita ce, ka samu wani da ka amince da shi da zai rika fassara maka abubuwan da aka fada a cikin harshen Hausa da Fulatanci.” Inji Sani.

A daidai lokacin da Sanata Sani ya yi wannan magana, ana bikin mauludin Tinubu a jihar Kano.

KU KARANTA: Hadimin Jonathan, ya yabi Tinubu, ya fadi lakanin doke shi a 2023

Shehu Sani ya ba Jigon APC, Tinubu muhimmiyar shawara bayan ya kai shekaru 69
Asiwaju Bola Tinubu a wani biki
Asali: Twitter

Daga baya Sani ya kira gamayyar da aka samu tsakanin Yarbawa da Fulani a bikin da YORULANI, ganin alakar gwamna Abdullahi Ganduje da Bola Tinubu.

Har ila yau, tsohon Sanatan ya yi martani ga masu nuna shakku game da shekarun Bola Tinubu, ya ce babu wani dalilin da za a ki yarda da shekarunsa.

Ku na da labari cewa wasu daga cikin manyan bakin da aka gayyata zuwa bikin jagoran APC na kasa, Bola Tinubu a garin Kano jiya ba su samu zuwa ba.

Hazo ya hana jirage tashi daga Garin Abuja zuwa jihar Kano. Hakan ya kawo wa mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, SGF, da wasu Ministoci cikas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng