Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

Babu wanda ya fi Tinubu dacewa a 2023 – Tsohon Gwamnan Arewa ya kawo karfafan dalilai

  • Kashim Shettima yana goyon bayan Bola Tinubu ya karbi mulki, ya ce ya fi kowa cancanta a Kudu
  • Daga cikin dalilan Shettima shi ne Tinubu ya rika marawa ‘Yan Arewa baya a zaben shugaban kasa
  • Sanatan na yankin Borno ta tsakiya ya ce Tinubu ne ya yi kokari wajen kafa jam’iyyar adawa a mulki

Abuja - Tsohon gwamnnan jihar Borno, Kashim Shettima ya ce idan za a yi adalci, ya kamata ‘Yan yankin kudu su fito da shugaban Najeriya a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce Sanata Kashim Shettima ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da magoya bayan Asiwaju Ahmed Bola Tinubu suka shirya.

Da yake jawabi a ranar Litinin, 17 ga watan Junairu, Kashim Shettima ya ce idan kuma mulki ya koma Kudu, babu wanda ya fi cancanta irin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ta’addanci: Masu kai wa 'yan bindiga bayanai sune babbar matsalar mu, El Rufai

Tsohon gwamnan na Borno ya ce Tinubu jagoran shugabanni ne, wanda ya dace ya mulki kasar nan.

Dalilan Kashim Shettima

“A lokacin da sa’annin Tinubu suka saida kansu a lokacin Obasanjo, shi kuwa Tinubu kokari ya yi wajen kafa jam’iyyar da za ta yaki PDP, ‘yan takararsa sun nuna irin kwarewarsa a siyasa.”
Tsohon Gwamnan Borno
Kashim Shettima a taron TSG Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

“Yadda Asiwaju Tinubu ya rika marawa ‘yan takarar shugaban kasa da suka fito daga Arewa a lokacin da wasu suke bangaranci, ya nuna shi mutum ne mai kishin kasa baki daya.”
“Hakurinsa ne ya kawo halin da muke ciki a yau, saboda haka sai mu tuna ya na bin mu bashi.” - Kashim Shettima.

Tinubu ya tsufa?

Jaridar ta ce Shettima ya soki masu zargin Tinubu yana boye shekarunsa, inda ya ce masu fadar wadannan maganganu sun jahilci irin kwazon ‘dan siyasar.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan siyasan Kudu na neman canza lissafin APC, Tinubu na hada-kai da abokan fada

Sanata Shettima yake cewa mulki ba karfin daga buhun siminti ba ne, ya ce abin da ake nema shi ne kaifin hankalin da shugaba zai iya kawowa mutane mafita.

Sanatan na Borno ta tsakiya yace shugabanci ya sha bam-ban da guje-guje a gasar Olympics.

Abin da ya dace Buhari ya yi

A 2015, ‘yan siyasa da ke da kudi a hannunsu sun nemi tikitin APC, amma Shettima yace Tinubu suka dage a kan sai Buhari, don haka ya kamata ayi halacci.

“Ina wadanda suka shigo jirgin Buhari daga baya? Mun san inda suka sa gaba a lokacin da Buhari ya zama ‘dan takarar APC. Su na ina a lokacin?”

- Kashim Shettima.

Taron Gwamnonin APC

An ji cewa gwamnonin APC sun yi zama, inda aka tsaida matsaya a game da zaben shugabanni. A watan gobe ake sa rai APC za ta fito da shugabanni na kasa.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso sun tsaya wasa, ‘Yan siyasa 2 sun bayyana niyyar tsayawa takara a PDP

Nasir El-Rufai, Yahaya Bello, Babagana Zulum, Abdullahi Umar Ganduje, Abubakar Atiku Bagudu da Dr. Kayode Fayemi su na wajen taron Gwamnonin da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng