Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Jama'a su na bukatar bincike mai tsauri kan alakar da ke tsakanin wasu gwamnoni da gagararren dan ta'adda, Bello Turji, bayan hotunan makusancin sa da gwamnonin sun bayyana kuma makusancin Turji ya yi fallasa a soshiyal midiya.

A wani hoto da Musa Kamarawa, akwai gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da na Sokoto, Aminu Tambuwal da kuma mataimakin gwamnan Sokoto, Mannir Dan Iya.

Zamfara da Sokoto jihohi 2 ne na arewa maso yamma da su ke fuskantar matsanancin farmakin 'yan ta'adda.

Hotunan ɗan ta'adda Turji tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura
Hotunan ɗan ta'adda Turji tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura. Hoto daga Premium Times
Asali: Facebook

Kamar yadda rahoton Daily Nigerian ya bayyana, an damke Kamarawa a Abuja a shekarar da ta gabata tare da wani Bashar Audu dan kasar Nijar da hodar iblis kuma ana zargin su na kai wa Turji ne da mutanen sa.

An kama Kamarawa a watan Satumba amma bidiyon tuhumar sa da 'yan sanda ke yi ya bazu ne makonni kadan da suka gabata.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Hotunan tarbar da El-Rufai ya yi wa Buhari a Kaduna bayan ya baro Gambiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin tuhumar sa, Kamarawa ya ce ya san Turji na tsawon lokaci.

“Turji babban aboki na ne, a koda yaushe mu na magana kuma mu na neman shawarar juna idan za mu yi aiki a lokuta da dama," wanda ake zargin ya ce.

Ya ce fitaccen dan bindigan ya na da masu gadi sama da dari wadanda ke dauke da makamai kuma ya bayyana wadanda ke kai wa Turji takalma, kayan sojoji, magunguna da sauran kayan bukata.

Alakar sa da Bafarawa

Binciken da Premium Times ta yi a Sokoto ya bayyana cewa, Kamarawa da ne ga babbar yayar tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarwa.

Sanannen abu ne cewa, Bafarawa jigon siyasar jihar Sokoto ne kuma ya kasance wanda ba ya yin shiru a kan ta'addanci. Ya na kira ga gwamnatin tarayya da ta sabunta tsarin ta na yaki da ta'addanci.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta titsiye Supo Shasore, tsohon kwamishinan Legas kan damfarar P&ID

Mahaifiyar Kamarawa ita ce babbar yayar tsohon gwamnan.

Matawalle da Kamarawa

Kamarawa wanda dan asalin karamar hukumar Isa na jihar Sokoto ne, ya san tudu da kwari tare da dajikan Sokoto ta gabas da Zamfara ta arewa, ballantana kauyukan da ke da iyakoki da Shinkafi da Isa.

Binciken da Premium Times ta yi ya bayyana cewa, Kamarawa ya na daga cikin wadanda Matawalle ya fara tuntuba bayan ya ci zabe a 2019, domin tabbatar da sasanci tsakanin sa da 'yan bindiga.

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Zamfara, wacce ta kasance mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan, ta ce an aike gwamnan wurin Kamarawa lokacin da ake son yin sasanci da 'yan bindiga.

"Duk da Bello Turji bai amince da sasancin ba, akwai 'yan bindigan da suka ajiye makaman su ta hanyar Musa Kamarawa.
"Ba mu taba sanin cewa tare su ke ba saboda a kodayaushe ya na shawartar mu da mu yi sasanci da su. Za ku iya shaida hakan saboda sun zo nan sun ajiye makamai kuma mun fuskanci zaman lafiya na wani lokaci," cewar jami'in gwamnatin da ya bukaci a boye sunan sa saboda ba a ba shi damar zantawa da manema labarai ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Sai dai kuma, an kasa tantance wasikar da ke yawo a soshiyal midiya na mukamin da gwamnan Zamfara ya bai wa Kamarawa a matsayin mai bada shawara na musamman, ta gaskiya ce ko bogi.

"Ba ni da tabbaci. Amma kamar kai, ni ma na ga wasikar. A ce gaskiya ne, hakan ya lalata kokarin sa na janyo 'yan ta'addan domin sasanci? Ko da gaskiya ce, Matawalle ya yi hakan ne da niyya mai kyau," yace.

Premium Times ta tattaro cewa, Kamarawa ne ya karba mahaifin Turji daga jami'an tsaro kuma ya mika shi ga 'yan ta'addan a watan Yuli bayan Turji ya sace mutum hamsin a matsayin martani kan kama mahaifin sa da 'yan sanda suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel