Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali

Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali

  • Kotu ba da umarnin tsare wani mai shekaru 35 da ake zargi da kashe mahaifiyarsa a jihar Ekiti
  • Wanda ake zargin Abiola Ayodeji ya doke mahaifiyar tasa ne da sanda sakamakon sabani da suka samu, lamarin da ya kai ga mutuwarta
  • Mai shari'a Titilayo Olaolorun, ta ce a ci gaba da tsare wanda ake karar a cibiyar gyara hali na Najeriya da ke Ado Ekiti, na tsawon kwanaki 30 kafin yan sanda su kammala bincike

Ekiti - Wata kotun majistare da ke Ado Ekiti ta amince da bukatar da aka gabatar gabanta na ci gaba da tsare wani dan shekaru 35 mai suna Abiola Ayodeji a gidan gyara hali, Ado Ekiti.

Dan sanda mai gabatar da kara, Bankole Olasunkanmi ne ya bukaci hakan, domin ba rundunar yan sanda damar kammala bincike.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Wa Matasa 3 Hukuncin Ɗaurin Shekaru 17 Saboda Satar N60,000 a Bauchi

Ana zargin Abiola da kashe mahaifiyarsa mai shekaru 75, Abiola Olaitan Florence, a ranar 11 ga watan Janairu a unguwar Ipole-Iloro a Jihar Ekiti.

Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali
Duniya kenan: Matashi mai shekaru 35 ya kashe mahaifiyarsa, ya gamu da fushin alkali Hoto: Thisday
Asali: UGC

Laifin da ya aikata ya saba wa sashe na 319 na kundin manyan laifuka na Jihar Ekiti na shekarar 2012.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take zartar da hukunci, Mai shari'a Titilayo Olaolorun, ta ce a ci gaba da tsare wanda ake karar a cibiyar gyara hali na Najeriya da ke Ado Ekiti, na tsawon kwanaki 30 kafin yan sanda su kammala bincike.

A jawabinsa ga yan sanda, Abiola Ayodeji wanda ya fito daga Ipole Iloro a karamar hukumar Ekiti ta yamma, ya ce ya samu sabani da mahaifiyarsa a wannan rana.

Sai ya kora ta da sanda sannan ya buga mata shi a kanta, lamarin da yayi sanadiyar mutuwarta. Daga bisani sai ya ajiye gawarta a daji.

Kara karanta wannan

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

An dage sauraron karar zuwa 21 ga watan Fabrairu, rahoton Aminiya.

Dan yaho da ya shiga hannu: Mahaifiyata ce tasa na kashe kani na don na yi kudi

A gefe guda, wani dan yaho mai shekaru 32, Afeez Olalere ya bayyana cewa shine ya kashe kaninsa domin yain kudin asiri bayan yan sandan jihar Lagas sun kama shi.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa wanda ake zargin wanda aka kama yayin wani aikin bincike a hanyar Itamaga da ke Ikorodu, Lagos, ya ce mahaifiyarsa ce ta karfafa masa gwiwar kashe kanin nasa.

Ya ce hakan ya kasance ne bayan wani boka da ta kai shi wajen sa ya fada masu cewa sai ya ba dodo jinin wani ya sha kuma dole mai shi ya kasance dan uwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel