Dan yaho da ya shiga hannu: Mahaifiyata ce tasa na kashe kani na don na yi kudi

Dan yaho da ya shiga hannu: Mahaifiyata ce tasa na kashe kani na don na yi kudi

  • Wani dan yaho mai shekaru 32, Afeez Olalere, ya shiga hannun yan sanda kan zargin kashe kaninsa
  • Wanda ake zargin ya fallasa cewa mahaifiyarsa ce ta kai shi wajen boka inda shi kuma ya nemi su kawo sassan jikin wani dan uwansa
  • Olalere ya ce da yawun mahaifiyarsa yayi amfani da kanin nasa domin ita ce ma ta bayar da gubar da aka sa masa a abinci ya ci ya mutu

Lagos - Wani dan yaho mai shekaru 32, Afeez Olalere ya bayyana cewa shine ya kashe kaninsa domin yain kudin asiri bayan yan sandan jihar Lagas sun kama shi.

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa wanda ake zargin wanda aka kama yayin wani aikin bincike a hanyar Itamaga da ke Ikorodu, Lagos, ya ce mahaifiyarsa ce ta karfafa masa gwiwar kashe kanin nasa.

Kara karanta wannan

Yadda za a cimma nasara wajen yaki da rashawa a Najeriya – IBB

Ya ce hakan ya kasance ne bayan wani boka da ta kai shi wajen sa ya fada masu cewa sai ya ba dodo jinin wani ya sha kuma dole mai shi ya kasance dan uwansa.

Dan yaho da ya shiga hannu: Mahaifiyata ce tasa na kashe kani na don na yi kudi
Dan yaho da ya shiga hannu: Mahaifiyata ce tasa na kashe kani na don na yi kudi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Olalere ya ce:

“Mahaifiyata ta kaini wajen wani boka wanda ya fada mani cewa idan ina so nayi nasara a aikin yaho, dole sai na sadaukar da rayuwar wani kuma dole ya kasance dan uwana na jini.”

Ya ci gaba da bayyana cewa ya bai wa kanin nasa guba ya ci, sannan ya mutu bayan mintuna 20 da shan shi.

A rahoton Daily Post, Olalere ya ce bayan sun cire sassan jikin da ake bukata, sai suka nade sauran suka kai dakin ajiyar gawa.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

“Abun da ke ciki shine sai ya hada magani da manyan yatsu, gashi da yatsunsa da kuma hoton fasfot.
“Don haka, muka koma gida sannan muka yi nazari a kai, sai mahaifiyata ta bayar da shawarar mu yi amfani da kanina tunda shi shekarunsa 21 ne kawai.
“Sai ta kuma kawo gubar wanda muka zuba masa a abinci. Ya mutu cikin mintuna 20 bayan ya ci abincin. Ni na yanka sassan jikin da ake bukata. Sai muka nade gawarsa sannan muka nufi dakin ajiyar gawarwaki.”

Mai laifi ya bayyana yadda ya kashe budurwarsa

A wani labarin kuma, wani mutum mai shekaru 31 a jihar Ogun, Tajudeen Monsuru ya tona cewa shi ya kashe budurwarsa, Mutiyat Alani don kudin asiri.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Tajudeen ya ce ya shake budurwar har lahira a ranar da ta zo gidansa sannan ya yanke kanta don yin asirin kudi.

Kara karanta wannan

Alheri danko ne: Bidiyon mai tallan pure water yana raba wa fursunoni kudi ya ja hankalin jama'a

Ya ce yan uwan budurwar basu san cewa ta kai ziyara gidansa ba sannan cewa babu wanda ya zarge shi a lokacin da ake neman ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel