Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina

  • Daga gardama kan Chelsea da Barcelona, an hallaka wani matashi a jihar Katsina
  • Mahaifin marigayin ya shigar da kara kuma an gurfanar da wanda ya kashe masa yaro a kotu
  • Alkali mai shari'a ta dage zaman da kimanin watanni biyu yayinda tace a garkame matashin da ake zargi a kurkuku

Gardama tsakanin masoya kungiyoyin kwallon Chelase da Barcelona ya sabbaba mutuwar wani matashi mai suna Saifullahi Abdullahi, a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina.

Abdullahi ya mutu ne bayan fadan da gardama ya haifar tsakaninsa da wani matashi Idris Yusuf, dan shekara 18.

Punch ta ruwaito cewa wannan abu ya faru ne ranar 18 ga Disamba, 2021.

Yan sandan sun bayyana cewa mahaifin Abdullahi ne ya kai kara ofishin yan sandan Danja ranar 20 ga Disamba, 2021.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Katsina
Mutum daya ya mutu sakamakon gardama kan Chelsea da Barcelona a Katsina
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gurfanar da Yusuf ranar Litinin gaban kotun majistare kam laifin kisan kai.

Lauyan yan sanda, Sajen Lawal Bello, ya bayyanawa kotu cewa Abdullahi ya yanke jiki ya fadi ne lokacin da fada ya kaure tsakaninsa da Yusuf.

Ya kara da cewa an garzaya da Yusuf asibiti kafin ya kwanta dama.

Alkali mai shari'a, Hajia Fadile Dikko, ta ada umurnin garkame Yusuf a magarkama yayinda ta dage zaman zuwa ranar 7 ga Maris, 2022.

Katsina: Masari ya yi umarnin bude dukkan gidajen mai da kasuwannin shanu a jihar

A wani labarin kuwa, Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya amince da gaggawar bude gidajen mai da kasuwannin shanu da a baya aka rufe saboda satar shanu da ta’addanci a jihar, Channels TV ta ruwaito.

Sai dai gwamnan ya bayar da umarnin ne bayan masarautu biyu da ke jihar sun tabbatar da yadda dagacin kauyukun suka tabbatar da sa ido kuma za su tabbatar ba za a bar wasu harkokin Sarakunan Fawa da sauransu ba.

Kara karanta wannan

Matashi da kanwarsa sun bayyana yadda tsawo da girman jikinsu ya zamo musu matsala

A wata takarda wacce sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ya sa hannu, ya ja kunne inda yace gwamnati za ta kara garkame su matsawar aka lura da wani ta’addanci a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel