Kotu ta yanke wa matasa 3 hukuncin ɗaurin shekaru 17 saboda satar N60,000 a Bauchi

Kotu ta yanke wa matasa 3 hukuncin ɗaurin shekaru 17 saboda satar N60,000 a Bauchi

  • Wata kotu mai zamanta a Bauchi ta yanke wa wasu matasa uku hukuncin daurin zaman shekaru 17 a gidan gyaran hali saboda fashi da makami
  • Matasan sun aikata laifuka biyu ne tun a shekarar 2018 inda suka yi wa wani Abdullahi Ahmodu duka da rauni sannan suka sace masa N60,000
  • Alkalin wadanda aka yanke wa hukuncin ya ce bai gamsu da hukuncin da aka yanke wa matasan ba kuma yana fatan zai daukaka kara ya samu sauki garesu

Bauchi - Wata babban kotu mai zaman ta a Bauchi, ta yanke wa wasu matasa uku hukuncin daurin shekaru 17 a gidan gyaran hali saboda aikata fashi da makami a shekarar 2018, The Punch ta ruwaito.

Mai gabatar da kara, M.M. Adamu ya ce mutane ukun da aka samu da laifi, Mua'azu Ya'u, Adamu Abdullahi, Awalu Babayo mazauna kauyen Gertogel a karamar hukumar Bauchi an gurfanar da su ne a Satumban 2018 kan aikata fashi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Dan Shehu Dahiru Bauchi ya fito takarar shugaban kasa na 2023

Kotu ta yanke wa matasa 3 ɗaurin shekaru 17 saboda satar N60,000 a Bauchi
Kotu ta yanke wa matasa uku hukuncin daurin shekaru 17 saboda satar N60,000 a Bauchi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Hakan kuma ya saba da sashi na 96 kuma sashi a 97 na Penal Code na Jihar Bauchi; Vol 1 na 2006 ya tanadi hukuncinsa a cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gurfanar da masu laifin, tare da wani Ruwa Abdullahi, wanda ake nema, 'kan kaiwa wani Abdullahi Ahmodu hari da adduna da sanduna, inda ya suma, bayan nan suka sace masa N60,000, kuma laifi ne wanda ya ci karo da sashi na (1) a da b na dokar fashi da makami na Jihar Bauchi.

Da ya ke yanke hukunci, Mai shari'a Abubakar ya yanke musu hukuncin shekaru biyu kowannensu a tuhumar farko, sannan ya yanke musu hukuncin shekaru 15 kowannensu a tuhuma ta 15 - duk kuma babu zabin biyan tara.

Lauya mai kare wadanda aka yanke wa hukunci ya ce bai gamsu ba

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa tsohon Sojan Najeriya hukuncin kisa ta hanyar Rataya

A yayin da ya ke martani kan hukuncin da aka yanke, lauyan wanda aka yanke wa hukuncin, Yakubu Maikasuwa, ya bayyana rashin gamsuwarsa kan hukuncin, yana mai cewa za su daukaka kara, yana fatan zai samu hukunci mai sauki.

Maikasuwa ya ce:

"Ba mu farin cikin ganin laifuka na karuwa."

Ya bayyana cewa abubuwa uku suna iya zama alheri ga wadanda ya ke karewa - shaidan da suka bada shaida, hujja da aka kare ta da shaidan da aka rubuta a ofishin yan sanda.

Ya ce:

"A wannan shari'ar, kotun kawai ta yi la'akari ne da abubuwan da (wadanda ake zargin suka fadi a ofishin yan sanda)."

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An tsinta gawar magidanci mai shekara 41 a otal, an cire wasu sassan jikin sa

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel