'Yan bindiga da ke assasa dokar zaman gida ta IPOB sun balle cocin Katolika a Onitsha

'Yan bindiga da ke assasa dokar zaman gida ta IPOB sun balle cocin Katolika a Onitsha

  • A ranar Talata ‘yan bindigan da ake zargin ‘yan awaren IPOB ne suka afka wa wata cocin katolika da ke Onitsha a jihar Anambra
  • An samu bayanai a kan yadda suka afka cocin ana tsaka da bauta inda suka tuhumi faston bisa tara jama’a yayin da Nnamdi Kanu ya ke hanyar zuwa kotu
  • Dama rahotanni sun nuna yadda Kanu ya gurfana gaban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata da safe wanda hakan yasa suka hana kowa fita a ranar

Onitsha, Anambra - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu son kafa kasar Biafra ne, 'yan awaren IPOB a ranar Talata suka afka wata cocin katolika da ke Onitsha, jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta tattaro bayanai a kan yadda ‘yan bindigan suka afka wa cocin yayin da ake tsaka da bauta sannan suka fara tuhumar faston dalilin sa na tara jama’a yayin da shugaban su, Nnamdi Kanu ya ke hanyar sa ta zuwa kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

'Yan bindiga da ke assasa dokar zaman gida ta IPOB sun balle cocin Katolika a Onitsha
'Yan bindiga da ke assasa dokar zaman gida ta IPOB sun balle cocin Katolika a Onitsha. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna yadda aka gurfanar da Kanu gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata da safe.

Daily Trust ta ruwaito, masu bautar sun shiga tashin hankali yayin da matasan suka afka cikin cocin da karfi da yaji.

Wata ganau ta shaida yadda fusatattun matasan suka fuskanci faston suna tuhumar sa inda ya yi musu dabara don shawo kawunan su.

Daily Trust ta ruwaito yadda ake zargin ‘yan IPOB din da kona wata keke Napep da suka gani a hanya sannan suka nada wa mai Napep din dukan tsiya.

Kamar yadda wani ganau ya shaida:

“Da safen nan na je cocin St Theresa ta Kalkuta Parish a Awada, wacce ta ke kusa da kwanar Ukaegbu da misalin karfe 5:30 na safe don yin bauta.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

“Muna tsaka da bautar sai wasu matasa da ake zargin ‘yan IPOB ne suka fado cocin. Suna rike da sanduna da fetur inda suka shiga kai tsaye cikin cocin.
“Suna isa gaban faston cocin, Rabaran Fr Joseph, suka tambaye shi abinda yasa ya tara jama’a yayin da shugaban su ya ke hanyar sa ta zuwa kotu. Daga ganin su a fusace suke".

Ta kara da cewa:

“Duk wani wanda ke cikin cocin ya tsere. Gaskiya an watse sosai don mutane sun taru a cocin don ko ni wani gida na shiga da ke kusa da cocin.
“Rabaran Joseph ya ce musu ya tara jama’a ne don a yi addu’ar fatan a sako Nnamdi Kanu. Ya yi amfani da dabara inda yace musu su na bayan Ndi Igbo ko basa bayan su? Daga nan ne suka daga kafa suka ce ashe duk mutanen cocin na su ne.
“Daga nan suka kira kowa don a koma a ci gaba da addu’o’i bisa yardar cewa ‘yan cocin ‘yan Biafra ne. Wasun mu a tsorace su ke don ba su iya komawa cocin ba. Bayan nan suka bai wa faston hakuri suka wuce.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

“Wannan taron matasan ne suka ga wani mai Napep a waje saboda ranar sun hana kowa fita. Suka kama shi suka zane sa tare da babbaka keken sa.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel