Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari

  • Wata mota ta yi mummunan hadari a wani yankin jihar Legas, lamarin da ake tunanin ya kashe mutane da yawa
  • Rahoton da muka samo ya ce har yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba har yanzu
  • Rahoton ya ce, wasu jami'an FRSC ne suka tare tankar mai a lokacin da hadarin ya afku nan take a hanyar

Legas - Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin da ya afku a garin Fidiwo dake jihar Ogun karshen babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Jaridar Punch ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Talata a lokacin da wata motar bas da ke dauke da kaya da ke kan hanyar zuwa Legas ta kutsa cikin wata tankar dizal.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

Hadarin mota ya kashe mutane a legas
Yanzu-Yanzu: Ana fargabar tankar mai ta kashe wasu mutane da dama a wani hadari | Hoto: infocus.com

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Oyo ne suka tare tankar ta mai a lokacin da hatsarin ya afku.

Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Ana yawan samun hadurra a jihar Legas, kwanakin baya akalla yara ‘yan makaranta 13 ne suka mutu a Legas a ranar Talata bayan da wata motar dakon kaya ta samu matsalar birki ta bi ta kansu, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaran suna dawowa daga makaranta ne lokacin da lamarin ya faru, Premium Times ta ruwaito.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Hadarin ya afku ne a kan titin Isheri, daf da ofishin ‘yan sanda na Ojodu yayin da yaran suka taso daga makaranta, inji rahoton Daily Trust.

A wani labarin, Ibrahim Jubril, daya daga cikin iyayen da aka tsinci gawar ‘ya’yansu a cikin wata mota da aka yi watsi da ita a Legas, ya magantu kan wannan mummunan lamari.

Kara karanta wannan

Tsagwaron barna: Wasu miyagun 'yan bindiga sun fille kan tsoho mai shekaru 65

Idan za a iya tunawa, an tsinci gawarwakin yara takwas da aka ce ‘yan shekara hudu zuwa shida ne a cikin wata mota da aka ajiye a kan titin Adelayo, Jah-Michael, a yankin Badagry a Legas, a ranar Asabar, 4 ga watan Disamba.

Da yake magana game da lamarin, Jubril wanda ya rasa ‘ya’ya hudu maza biyu mata biyu, ya ce babu wanda ya san yadda yaran suka shiga cikin motar, inji rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel