Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka 4, wasu sun jigata

  • Rayuka hudu sun salwanta yayin da wasu suka jigata bayan 'yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta a kauyen Dikko da ke karamar hukumar Giwa
  • 'Yan ta'addan sun bayyana a babura inda suka bude wa 'yan bikin wuta, lamarin da ya gigita jama'a har suka fara gudun neman tsira
  • A halin yanzu, wasu daga cikin wadanda suka samu raunin an mika su asibiti inda suke karbar taaimakon masana kiwon lafiya

Giwa, Kaduna - A kalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu masu tarin yawa suka jigata bayan 'yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta a jihar Kaduna, TVC News ta ruwaito.

'Yan ta'addan sun bayyana a babura inda suka tsinkayi wurin bikin da ake yi a kauyen Dikko da ke karamar hukumar Giwa ta jihar a ranar Juma'a kuma suka dinga harbe-harbe babu kakkautawa, lamarin da ya tsorata jama'a.

Kara karanta wannan

Zamfarawa sun yi zanga-zanga saboda tsanantar kashe-kashe a yankunan su

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka hudu, wasu sun jigata
Kaduna: 'Yan ta'adda sun bude wa 'yan biki wuta, sun halaka hudu, wasu sun jigata. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mutum hudu daga cikin 'yan bikin aka halaka yayin da wasu suka jigata kuma aka mika su asibiti domin samun taimakon gaggawa.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar.

A wani lamari mai kama da hakan, kwamishinan ya sanar da yadda 'yan ta'adda suka tsinkayi Makarfi da ke Kufana a karamar hukumar Kajuru da ke jihar kuma suka kashe mutum daya a kauyen, TVC News ta ruwaito hakan.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya aike da sakon ta'aziyyar sa ga iyalan wadanda lamarin ya ritsa da su, ya yi kira ga hukumomin tsaro da ke jihar da su tsananta kokari wurin tabbatar da an damke 'yan ta'addan.

Kaduna: Jama'a suna gudun hijira bayan kutsen 'yan ta'adda a kauyen Damari

Kara karanta wannan

An kashe mutane 5, an kona gidaje sakamakon arangama tsakanin makiyaya da manoma a Ogun

A wani labari na daban, daruruwan jama'a mazauna yankin Damari da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna suna gudun hijira bayan 'yan ta'adda a babura sun kutsa yankunan su a safiyar Lahadi.

Mazauna kauyen sun sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun bibiyi mambobin kungiyar dan bindiga Malam Abba ne, wanda rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a 2020 suka tabbatar da cewa dan Boko Haram ne.

Ibrahim Hassan, wani mazaunin Damari, wanda ya bar yankin, ya sanar da Daily Trust cewa 'yan bindiga sun tsinkayi yankin wurin karfe goma na safiyar Lahadi, inda ya kara da cewa sun fara gudun ne bayan jin harbin bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel