Tashin Hankali: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'iza

Tashin Hankali: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'iza

  • Mutane na tsaka da Jana'izar wata mata, ba zato yan bindiga suka kunno kai, suka bude musu wuta kan mai uwa da wabi
  • Ɗaya daga cikin waɗan da suka tsira, yace maharan sun zo kan motocin Sienna guda Bakwai, suka tarwatsa kowa ya nemi hanyar tsira
  • Yace yan bindigan sun cinna wa gidan mutumin da akai wa rasuwar wuta, amma Allah ya sa bai ƙone ƙurmus ba

Anambra - Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki wurin Jana'iza a Ezinifitte, karamar hukumar Nnewi South, jihar Anambra, inda suka tarwatsa mutanen da suka halarci wurin.

Ɗaya daga cikin baƙin da suka halarci jana'izar, wanda ya zanta da Dailytrust yace, Jana'izar ta ƙare babu shiri, bayan maharan sun mamaye yankin.

Mutumin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace yan bindigan sun kai harin ne bayan samun labarin wani babban mutum a yankin yana bikin birne yar uwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Matawalle ya bayyana mutanen dake rura wutar ta'addanci a Zamfara

Yan bindiga
Tashin Hankali: Yan bindiga sun bude wa mutane wuta ana tsaka da Jana'iza Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace wasu daga cikin mazauna yankin sun gargaɗe shi kan cewa ba zasu lamurci kawo wasu jami'an tsaro yankin ba.

Yadda lamarin ya faru a wurin Jana'iza

Mutumin yace:

"Lokacin da yan bindigan suka samu labarin cewa wani ya kawo jami'an tsaro yankin, sai suka shirya a motocin Sienna bakwai suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi."
"Mutumin dake kokarin birne yar uwarsa da kuma jami'an tsaron sun tsira. Amma yan bindigan sun daɗe a wurin suna harbe-harben bindiga."
"Baki ɗaya mutanen da suka halarci bikin Jana'izar sun ari na kare domin tsira da rayuwarsu, wasu suka yi cikin jeji, wasu suka afka gidajen mutane dake kusa."

Shin sun kashe mutane a harin?

Majiyar ya ƙara da cewa maharan sun kwashe baki ɗaya motocin mahalarta jana'izan, kuma suka cinna wa gidan Wuta, amma bai ƙone duka ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Saurayi ya kashe mahaifin budurwarsa ta hanyar daɓa masa wuƙa yayin da ya kama su suna tsakar 'soyewa' a gidansa

"Duk waɗan da suka yi cikin jeji can suka kwana, sai da safe suka dawo, amma mu da muka shiga gidajen mutane, sai da yan bindigan suka fito da mu, sannan suka shaida mana ba ruwansu da mu."
"Idan kaga mutanen sai ka tsorata, suna ɗauke da muggan makamai, na ɗauka ranar zan mutu."

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga, yace hukumar yan sanda ba ta da masaniyar kai hari wani yankin jihar.

A wani labarin na daban kuma Kaftin Hassan, Wani Gwarzon sojan Najeriya da ya hallaka dandazon mayakan Boko Haram shi kaɗai

Akwai dakaru da dama a rundunar sojojin Najeriya da suka bada gudummuwa wajen yaƙi da ta'addanci fiye da tsammani amma ba kowa ya san su ba.

Mun tattaro muku takaitaccen bayani kan Kaftin Hassan, sojan da shugaban Boko Haram yasa kyautar miliyan N10 ga duk wanda ya kashe shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel