Sarkin Yaki: Gwarzon Sojan Najeriya, wanda ya hallaka dandazon mayakan Boko Haram shi kaɗai

Sarkin Yaki: Gwarzon Sojan Najeriya, wanda ya hallaka dandazon mayakan Boko Haram shi kaɗai

  • Akwai dakaru da dama a rundunar sojojin Najeriya da suka bada gudummuwa wajen yaƙi da ta'addanci fiye da tsammani amma ba kowa ya san su ba
  • Mun tattaro muku takaitaccen bayani kan Kaftin Hassan, sojan da shugaban Boko Haram yasa kyautar miliyan N10 ga duk wanda ya kashe shi
  • Mutanen garin Damboa dake jihar Borno, sun raɗa wa Hassan suna Sarkin yaƙi, saboda jajircewarsa da kuma rashin tsoro

Borno - Akwai gwarazan dakarun sojin Najeriya da suka bada rayuwarsu domin kwanciyar hankalin yan ƙasa amma ba kowa ya san su ba.

Jaridar Punch ta rahoto wani babban gwarzon soja a Najeriya, wanda ya addabi mayaƙan kungiyar ta'addanci Boko Haram, Kaftin MM Hassan.

Sarkin yaki, Kaptin Hassan
Sarkin Yaki: Gwarzon Sojan Najeriya, wanda ya hallaka dandazon mayakan Boko Haram shi kaɗai Hoto: Punch FB Fage
Asali: Facebook

A shekarun baya, sai da tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Sheƙau, wanda aka kashe, ya saka miliyan N10m kan duk wanda ya kawo masa kan MM Hassan.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a yaki da rashin tsaro - Tinubu

Ga mutanen garin Damboa dake jihar Borno, Marigayi MM Hassan, soja ne da bai san juya wa ba kuma koda yaushe a shirye yake ya shiga filin yaƙi.

Mazaunan wannan gari a Arewa maso gabashin Najeriya sun raɗa masa suna da, Sarkin Yaki' kasancewarsa gwarzo na gaban kwatance.

Meyasa Sheƙau yasa miliyan N10m a kansa?

A cewar wani masani kan harkokin tsaro, Zagaola, shugaban Boko Haram na wancan lokacin Abubakar Shekau, ya saka wa mayakan sa miliyan N10m kan Kaftin Hassan, ne sabida barnar da yake musu.

Zagaola ya rahoto cewa an kashe Kaptin Hassan ne a filin yaƙi a ranar Laraba, 5 ga watan Janairu, 2018, shekaru kusan hudu kenan da suka shude.

Legit.ng Haua ta gano cewa MM Hassan ya riga mu gidan gaskiya ne yayin da suke fafatawa da yan ta'adda a garin Damboa, dake jihar Borno.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa na yarda zan lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Tinubu

Yanzu shekara kusan hudu kenan da kwanta daman mazan fama irin su Hassan, amma har yau yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabas bai ƙare ba.

A wani labarin kuma Ministan cikin gida ya umarci gandurobobi su bindige duk wanda ya yi yunkurin fasa gidan Yari a inda ko shurawa ba zai yi ba

Ministan ya bayyana cewa duk wani hari da aka kaiwa gidan Gyaran Hali tamkar ƙasar Najeriya ce aka kaiwa hari, kuma ba za'a sake barin haka ta sake faruwa nan gaba ba.

A cewar Mista Rauf Aregbesola, kai hari gidajen Yari tamkar ƙunar baƙin wake ne, dan haka duk mai hannu a haka bai dace ya rayu ba bare ya bada labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel